1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata na limanci a sabon masallacin Berlin

Gazali Abdou Tasawa
June 17, 2017

A kasar Jamus a jiya Jumma'a ne aka gudanar da bikin bude wani sabon masallacin Jumma'a a birnin Berlin wanda aka yi wa suna Ibn Rushd-Goethe inda mata ke ladanci da limanci.

https://p.dw.com/p/2erAG
Deutschland Eröffnung liberale Moschee in Berlin
Syran Ates limamiyar sabon masallacin Berlin na huduba gaban mamuHoto: picture-alliance/dpa/M. Gambarini

A kasar Jamus a jiya Jumma'a ce aka gudanar da bikin bude wani sabon masallacin Jumma'a a birnin Berlin. Masallacin wanda aka yi wa suna Ibn Rushd- Goethe wanda wasu mata Musulmi bakwai suka dauki dawainiyar ginashi, na da burin samar da a cewarsu wata sabuwar fuskar Muslunci da kuma ta sha bam-bam da masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama. Wasu daga cikin sabbin sauye-sauyen da jogoran wannan masallaci suka fito da su, sun hada da mika limanci da ma ladanci ga mata tare da hade mata da maza a cikin sahu guda a lokacin gudanar da sallah.

Ani Zonneveld  wata 'yar asalin kasashen Amirka da Malesiya ita ce ke ladanci a wannan masallaci, kana Seyran Ates ita ce limami wannan masallaci, ta kuma yi karin bayani kan tsarin wannan masallaci nasu tana mai cewa:

Ta ce "Mu na huduba kan maudu'in da ya shafi kaunar juna , kuma nan ba za ka ji hudubar adawa da Demokradiyya ba, domin ba mu amince da dokokin shari'a kamar yadda wasu ke tafiyar da su ba a yanzu ba, mu muna goyon bayan dokar kare 'yancin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ne"

Bikin bude masallacin ya samu halartar wakillan Kiristoci da na Yahudu.