Mataimakin shugaban Amirka ya kai ziyarar bazata Iraki
December 18, 2005Talla
Mataimakin shugaban Amirka Dick Cheney ya kai wata ziyarar ba zata a Iraqi. An gudanar da shirye-shiryen kai wannan ziyara cikin sirri, abinda da alama ya zowa FM Iraqi Ibrahim al-Jaafari da bazata. Bayan ya gana da jami´an gwamnati mista Cheney ya kuma tattauna da kwamandojin sojin Amirka a yankin nan na tsaro da ake kira Green Zone dake birnin Bagadaza. Ziyarar ta sa ta zo ne a daidai lokacin da sabbin tashe tashen hankulan da suka barke a Iraqi, suka yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 17. Shugabannin ´yan sunni da shi´a sun yi kira da a kwantar da hankali kana kuma a guji abin da suka kira ta da zaune tsaye da zai rarraba kawunan ´yan kasar bayan zaben gama gari da aka gudanar cikin makon jiya.