1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan Gwamnatin Jamus Domin Hana Billar Rikice-Rikice

May 13, 2004

A karkashin wani shirin aiki da ta gabatar gwamnatin Jamus zata kara karfafa matakanta na kandagarkin tashe-tashen hankula a dukkan sassa na duniya

https://p.dw.com/p/Bvjd
Sojan kiyaye zaman lafiya a kasar Kongo
Sojan kiyaye zaman lafiya a kasar KongoHoto: AP

Jamus zata kara yin hobbasa a kokarinta na hana billar rikice-rikice akan lokaci a dukkan sassa na duniya. Dangane da haka gwamnati a birnin Berlin ta tsayar da wani kuduri wanda ya tanadi matakai na lumana domin kandagarkin yake-yake tare da hadin kan MDD, kamar yadda aka ji daga bakin Kerstin Müller, karamar minista a ma’aikatar harkokin wajen Jamus, wadda ta ce kasar zata dauki wannan matakin ne domin bin saun kasashen Sweden da Birtaniya. Ta ce muhimmin abin dake akwai shi ne neman hanyoyi na laluma domin hana billar rikice-rikice da kuma warware wadanda ake fama da su a siyasance. Babbar manufar da za a sa gaba shi ne bin diddigin rikice-rikicen daga tushensu ta yadda za a gano dalilansu ta fannoni na siyasa da tattalin arziki da zamantakewar jama’a da kewayen dan-Adam saboda ta haka ne kawai za a iya shawo kansu. Wadannan batutuwa sune ainifin madogarar shirin da gwamnati ta tanadar bisa manufa. A baya ga manufofin ketare da na tsaro da kuma na taimakon raya kasa, wajibi ne a karfafa huldodin tattalin arziki da na kudi da kuma na kewayen dan-Adam domin kandagarkin yake-yake da sauran rikice-rikicen da suka zama ruwan dare a duniya yanzu haka. Da zarar an kawo karshen rikici to kuwa wajibi ne a dauki nagartattun matakai na sake gabatar da tsare-tsaren da zasu taimaka wajen hana billar wani sabon rikicin. Tun abin da ya kama daga shekarar 1999 Jamus ta tura kwararrun masana al’amuran zaman lafiya kimanin 167 zuwa yankunan da aka sha fama da rikice-rikice a cikinsu domin taimakawa wajen sake farfado da ayyukan farar fula a cikin ruwan sanyi. A shekara ta 2002 an kirkiro wata cibiya ta kasa da kasa akan ayyukan kiyaye zaman lafiya, inda ake ba da horo ga kwararrun ma’aikata na MDD da Kungiyar tsaro da Hadin Kai a Nahiyar Turai OSCE a takaice. A baya ga haka gwamnati a fadar mulki ta Berlin ta kara karfafa taimakon da take bayarwa ga kasashen dake canja manufofinsu a bangarorin demokradiyya da tsaro da kuma ayyukan doka. Tun dai a shekara ta 2000 ne gwamnati ta cimma daidaituwa da kungiyoyi masu zaman kansu akan matakan riga kafin rikice-rikice wadanda za a fara aiwatar da su a yanzun. Jamus zata ba da cikakkiyar goyan baya a matakan nan na yi wa makamai da harsasai tambarin da zai yi bayanin inda suka fito ta yadda za a iya bin diddiginsu a ko’ina a duniya. A bangaren kewayen dan-Adam kuwa a halin yanzu haka fadar mulki ta Berlin tana rufa wa hukumomin kula da al’amuran koguna a nahiyar Afurka baya saboda ganin an yi raba daidai wajen cin amfanin wadannan koguna. Jamus ta yanke wannan kuduri ne saboda mayar da martani a kan sabbin matsalolin da duniya ke fama da su kama daga ayyukan ta’adda zuwa ga yake-yake na basasa kamar a Sudan a yanzu haka ko kuma wargajewar tsarin gwamnatin tsakiya kamar yadda lamarin yake dangane da Somaliya.