1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IOC Olympia Zensur

von Hein, MatthiasJuly 31, 2008

Hukumomin China sun ɗauki matakan tace rahotannin da za a riƙa yaɗawa ta yanar gizo a lokacin wasannin Olympics

https://p.dw.com/p/Eo2h
Filin wasan Olympics a BeijingHoto: AP Images


Tun bayan da labari ya fito fili cewar kasar China na da niyyar haddasa cikas a harkar yada labarai ta yanar gizo lokacin wasannin duniya na olympics a Beijing kwamitin wasannin olympics na kasa da kasa ya shiga wani hali na kaka-nika-yi, saboda kwamitin na da cikakkiyar masaniya a game da aniyar mahukuntan Chinar ta tace rahotannin da za a rika yadawa ta yanar gizo, kuma abin mamaki yayi na'am da hakan.


Ko da yake a cikin wani rahoton da gidan rediyon BBC ya bayar ya nuna cewar Chinar ta ba da damar bude shafinsa na yanar gizo da ake gabatarwa da harshen Chanisanci, amma shafin yanar gizo na tashar DW da na kungiyoyin kare hakkin dan-Adam kamar su Amnesty International an toshensu baki daya. A cikin wata hira da DW tayi da shi, darektan kungiyar wasannin olympics ta Jamus Michael Vesper yayi kira ga mahukuntan Chinar da su yi watsi da wannan mataki nasu su kuma bai wa dukkan 'yan jarida damar yin amfani da yanar gizo wajen yada rahotanni. Vesper ya kara da cewar:

Vesper:

"Ban ki ba idan kowace kasa dake doron duniyar nan tamu ta toshe wasu shafuka na yanar gizo wadanda ba su da ce ba, kamar dai hotuna na batsa da farfagandar zazzafan ra'ayin wariya. Amma fa wannan matakin bai shafi ayyukan kungiyar Amnesty ko sashen Chanisanci na tashar DW ba. Shi shafin yanar gizo wani bangare ne dake taimaka wa 'yan jarida a matakansu na bincike da bin bahasi, a saboda haka wajibi ne China ta dakatar da wannan mataki nata."


Ita ma kungiyar 'yan jarida ta Jamus tayi Allah Waddai da matakin toshe shafin na yanar gizo, inda wani da ake kira Hendrik Zörner daga kungiyar ke cewar wannan babbar barazana ce ga alkawarin da China tayi na bai wa 'yan jarida cikakkiyar dama ta gudanar da ayyukansu lokacin wasannin na olympics. Hendrik Zörner ya kara da cewar:

Zörner:

"Abin mamaki ne ganin yadda mahukuntan China ke kokarin yin cikas ga ayyukan yada labarai. Wannan wani yunkuri ne na tace rahotanni da muke Allah Waddai da shi."


A hukumance dai Chinar bata fito fili ta hakikance gaskiyar niyyarta ta yin cikas ga manyan kafofin yada labarai na kasa da kasa wajen gudanar da ayyukansu ta yanar gizo ba, inda suka rika ikirarin cewar wai mai yiwuwa a fuskanci wata matsala ta fasahar gudanarwa. A yanzun dai dab da fara wasannin na olympics rikicin yayi tsamari kuma ana zargin kkwamitin olympics na kasa da kasa da kasancewar tana da cikakkiyar masaniya game da lamarin. To sai dai kuma duk da wannan cece-kucen da aka yi darektan kungiyar wasannin olympics ta Jamus Michael Vesper na goyan bayan bai wa China damar karbar bakuncin wasannin da aka yi, wanda yake gani wani ci gaba ne ba da za a sake mayar da hannun agogo baya game da al'amuran China ba.