1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan yaƙi da ta'addanci a nan Jamus.

YAHAYA AHMEDSeptember 5, 2006

Ministocin harkokin cikin gida na tarayya, sun tsai da shawarar ɗaukan wasu tsaurararn matakai na kafa wata ma'adana ta tattara bayanai kan 'yan ta'adda, a wani yunƙurin ƙago sabbin hanyoyi na yakan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/BtyM
Ministan harkokin cikin gida na tarayyar Jamus, Wolfgang Schäuble
Ministan harkokin cikin gida na tarayyar Jamus, Wolfgang SchäubleHoto: AP

A taƙaice dai za a iya cewa an yanke shawarar kafa ma’adanar tattara labarai kan ’yan ta’adda ne cikin gaggawa, ba tare da yin nazari mai zurfi kan sakamakon da wannan matakin zai ikya janyowa ba. Bayan yunƙurin da aka yi na ta da bamamai cikin jiragen ƙasa a nan Jamus da bai ci nasara ba ne dai ’yan siyasa suka yi ta jawabai na neman a tsananta matakan tsaro, tare da bai wa ’yan sanda da sauran kafofin tsaro ƙarin iko, wajen gudanad da bincikensu. Amma dai sanin kowa ne dai, babu wata doka a nan duniyar, wadda za ta iya hana ’yan ta’adda kai hare-harensu idan sun ɗau niyyar yin hakan.

A kan wannan batun dai, ministan harkokin cikin gida Wolfgang Schäuble ma ya amince da cewar, ko da an tattara bayanai kan duk wani ɗan ta’adda a nan Jamus, hakan ba zai iya hana su gudanad da ɗanyen aikinsu ba. Amma tun da yunƙurin ta da bamabamai a cikin jiragen ƙasan ya ci tura, kamata ya yi a bai wa jami’an tsaro damar ɗaukan matakan yin riga kafi.

To sai dai, wasu ’yan siyasan, musamman masu neman a ɗau tsauraran matakai a nan Jamus tun lokacin harin ƙunan baƙin waken ran 11 ga watan Satumba na shekara ta 2001, sun yi amfani da wannan lokacin ne wajen cim ma burinsu. Amma za a iya lura da cewa, tun da aka kai wannan harin da kuma tsauraran matakan da wasu ƙasashen suka ɗauka bayan haka, ba a sami sassaucin hare-haren ba. A daura da haka ma, sai ƙaruwa suka yi ta yi.

Babu shakka, wajibi ne a ɗau barazanar ta’addancin ƙasa da ƙasa da muhimmanci. Saboda babu wata ƙasar da ta tsira daga wannan barazanar. Wasu daga cikin ’yan harin ƙunan baƙin waken ran 11 ga watan Satumba ma, daga nan Jamus suka tsara shirye-shiryensu kafin su tashi zuwa Amirka su gudanad da wannan ɗanyen aikin.

Wannan kawai ma, ya isa ya hujjanta kiran da ake yi na kafa cibiyar tattara bayanan kan ’yan ta’adda. Sai dai, a nan Jamus, tsarin ɓangarorin siyasar da ake da shi ne ke gindaya wa duk wani yunƙuri ɗaukan matakai na bai ɗaya shinge. Yayin da jam’iyyun ’yan mazan jiya ke neman a ƙara ɗaukan tsauraran matakai, ’yan jam’iyyun gurguzu na SPD da Greens da kuma FDP masu sassaucin ra’ayi, gani suke yi waɗannan matakan na take ’yancin zaman walawala da ’yan ƙasar nan ke da shi. Ko wane ɓangare dai ya dage ne wajen kare matsayinsa.

Abin da ya fi muhimmanci ga ’yan ƙasar nan, wanda kuma ya kamata ’yan siyasa su yi la’akari da shi, shi ne samar da yanayi na tabbataccen halin tsaro, tare da tsara matakan kau da duk wata barazana ga lafiyar jama’a. To amma tsai da shawarar kafa wata ma’adana ta tara bayanai kan ’yan ta’adda cikin gaggawa kawai, bayan doguwar ce-ce ku cen da ’yan siyasa suka yi ta yo da juna bai wadatar ba. Mai yiwuwa ma, wani ya iya ɗaukaka ƙara gaban kotun kundin tsarin mulkin ƙasa, saboda yana ganin wannan tsarin ya saɓa wa ƙa’idojin kundin.