1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan yaƙi da talauci

October 23, 2009

Har yau babu wata alamar dake nuna cewar za a cimma nasarar yaƙi da talauci a duniya nan da shekara ta 2015

https://p.dw.com/p/KDnF
Shin akwai mafita daga matsalar talauci?

Ƙasashe masu ci gaban masana'antu sun yi alƙawarin ware cent bakwai daga kowane ciniki na Euro goma da suka yi don ba da taimako ga ƙasashe masu tasowa. Kuma ko da yake wannan ba abu ne da ya taka kara ya karya ba, amma fa ba za a cimma wannan manufa ba, musamman ma ta la'akari da rikicin kuɗin da aka fuskanta baya-bayan nan.


Wani abin lura dai shi ne ƙasashen da suka fi wadatar arzƙi su ne kuma ke ba da taimako mafi ƙanƙanta bisa manufa. A duk lokacin da suka lura cewar lissafin jumullar abin da suke samarwa a shekara yana da tsoka sai riƙa noƙewa. An ji daga Jeffrey Sachs ƙwararren masanin al'amuran tattalin arziƙi yana mai bayanin cewar:


:"Ƙasashen Turai sun ce zasu cika alƙawarin da suka yi na taimakon kashi sufuli da ɗigo bakwai cikin ɗari nan da shekara ta 2015. Hakan zai zama babban ci gaba. Mai yiwuwa ƙasashen na Turai su cika alƙawarin nasu. Amma fa an daɗe ana gafara sa ba ma ganin ko ƙaho. A saboda haka ake tababa ko da gaske suke yi kuma zasu cika alƙawari?"


Shi dai Jeffrey Sachs, ƙwararren masanin tattalin arziƙi yayi shekaru da dama yana ba wa Majalisar Ɗinkin Duniya shawara akan manufofinta dangane da shekaru na 2000. Kuma ya sha nanata cewar kashi sufuli cikin darin fa bai taka kara ya karya ba, saboda duka-duka bai wuce cent bakwai akan kowane Euro goma ba. Su ma ƙasashen Amurka da Japan sun yi irin wannan alƙawari, amma fa a halin da ake ciki yanzun yawan taimakon da suke bayarwa bai kai ma ko kashi sufuli da ɗigo uku cikin ɗari ba. Bisa ga ra'ayin Imme Scholz darektar cibiyar manufofin raya ƙasa ta Jamus dai ba yawan kuɗin ne ke da muhimmanci ba, sai dai yadda za a aiwatar da su. Wato dai a taƙaice ba girin-girin ba tayi mai:


"Abu na uku da ya kamata a ankara da shi shi ne cewar ci gaba ba wata haja ce da za a iya sayenta ba. Wannan shi ne abin da muka lura da shi tsawon shekaru 40 da suka wuce. Gabatar da kuɗi da tura ƙwararru kawai ba zai wadatar wajen samar da ci gaba ba sai an haɗa da ba da ƙwarin guiwa ga ƙasashe masu tasowa domin su dage kan ƙafafuwansu."


Bisa lura da haka ne cibiyar nazarin manufofin raya ƙasa ta duniya ta gabatar da nata jadwalin a game da manufofin raya ƙasashe masu tasowa, tana mai ba da la'akari da wasu abubuwa dake taka raya kamar dai taimako na kai tsaye da cinikayya da zuba jari da guje-gujen hijira da kewayen ɗan-Adam da tsaro da kuma fasaha. Babu kuma ɗaya daga cikin gaggan ƙasashen dake ba da taimako da cimma nasara akan waɗannan manufofi.


Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu