1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

270810 Frankreich Roma

Halimatu AbbasAugust 27, 2010

Faransa na ci gaba da korar 'yan ƙabilar Roma.

https://p.dw.com/p/OyAm
'Yan Roma a matsuguninsu na asali.Hoto: AP

Ana ci gaba da korar 'yan ƙabilar Roma daga ƙasar Faransa domin komar da su gida a ƙasashen Rumeniya da Bulgeriya. Gwamnati a birnin Paris tayi watsi da damuwar da hukumar zartaswa ta ƙungiyar tarayyar Turai ta nunar a game da wannan mataki. Su kansu Faransawan dai kawunansu ya rabu biyu akan wannan batu.

Bisa ga dukkan alamu ba wani abin da ke ci wa Shugaba Nikolas Sarkozy na ƙasar Faransa da majalisar ministocinsa tuwo a ƙwarya a game da sukan lamirinsa da ake yi dangane da matakan da yake ɗauka akan 'yan ƙabilar Roma. Gwamnati ta yi ko oho da wannan suka ya-Alla a cikin gida ne ko daga ƙetare.

A jiya Alhamis sai da aka sake kwasar wasu 'yan ƙabilar Roma su kimanin metan da hamsin daga biranen Lyon da Paris zuwa ƙasar Rumeniya. A wannan karon ma sai da mahukuntan Faransa suka yi iƙirarin cewar mutanen da aka koran sun bar Faransa ne bisa raɗin kansu kuma a saboda haka aka ba wa kowane daga cikinsu taimakon kuɗi na Euro 300. Kazalika a halin da ake ciki yanzu kuma, kamar yadda aka saba gani kusan a kowace rana, an sake rushe wani sansanin na 'yan Roma. A wannan karon a garin Lille da ke arewacin Faransa. An rushe tantin da mutane kimanin 75 ke fakewa a cikinsa, inda suka wayi gari ba su da muhallin zama, kuma ga alamu nan ba da daɗewa ba za a kore su daga Faransa. Akan haka shugaban ƙungiyar bishop-bishop na Faransa Cardinal Andre Vingt-Trois yake cewa: "A ganina hakan ta haifar da wani gurɓataccen yanayi tsakanin jama'a. Kowane ɓangare na ƙalubalantar ɗan uwansa. Abin ya zama tamkar gasa ne tsakanin masu fafutukar tabbatar da tsaro da masu ƙoƙarin nuna halin sanin ya kamata."

Frankreich fliegt weitere Roma aus
'Yan Roma da ke barin FaransaHoto: picture-alliance/dpa

Shi dai babban limanin kirista ɗin dai ba shi ne kaɗai wani wakilin coci da ke tofin Allah tsine akan matakin da Sarkozy yake ɗauka akan 'yan Roma ba. A ma ranar Lahadi da ta wuce sai da wani pasto daga arewacin Faransa ya yi wa shugaban Faransar addu'ar samun ciwon zuciya a bainar jama'a. Ya ce dalilin haka shi ne yadda gwamnati ta lashi takobin saka ƙafar wando ɗaya da 'yan Roma ba gaira ba dalili. Ya kuma sake mayar da lambar yabo ta ƙasa da ya samu zuwa ga ministan cikin gida don bayyana adawarsa da wannan mataki. Tuni ma dai da yawa daga jami'an siyasa suka fara batu a game da manufofin ƙyamar baƙi na gwamnatin Faransa. Shi kansa sakataren ƙasar Rumeniya mai kula da al'amuran 'yan Roma, sai da ya fito fili yana mai bayyana ra'ayinsa game da lamarin ba tare da wata rufa-rufa ba. Ya ce:"Doka ba ta tanadar wa wani ikon hana wani ɗan nahiyar Turai yin tafiye-tafiye tsakanin ƙasashen nahiyar ba. Ba shakka wajibi ne ayi ƙoƙarin magance talauci. Mai yiwuwa talauci shi ne ɗaya daga cikin dalilin da suka sanya 'yan ƙasar Rumeniya da ma na wasu ƙasashen Turai ke ƙaura daga ƙasashensu tare da fatan kyautata makomar rayuwarsu a wasu wuraren dabam. Za mu mayar da hankalinmu akan wannan batu."

Brice Hortefeux Innenminister Frankreich
Brice Hortefeux, ministan cikin gidan Faransa.Hoto: AP

Amma fa ita gwamnatin Faransa har yau tana nan akan bakanta, inda ministanta na cikin gida Brice Hortefeux ya ƙara kare matakin gwamnatin da kuma danganta 'yan Roma da ƙaruwan miyagun laifuka a Faransa. Tun dai abin da ya kama daga farkon wannan shekara zuwa yanzun an mayar da 'yan Roma kimanin dubu tara zuwa ƙasashen Rumeniya da Balgeriya.

Mawallafi:Ahmad Tijani Lawal

Edita:Halima Balaraba Abbas