1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin hana faduwar kudin Euro

May 11, 2010

Kasashen kungiyar hadin kan Turai sun gabatar da matakan hana fadi-tashin kudin su na Euro

https://p.dw.com/p/NLVI
Alamar kudin Euro na kasashen TuraiHoto: AP

Kasashen kungiyar Turai sun gabatar da wani shiri da ba'a taba ganin irin sa ba, na hana durkushewar kasashe masu amfani da takardun kudin Euro. Kasashen sun dauki wannan mataki ne domin hana fadi-tashin kudin na Euro a kasuwannin hada-hadar kudi a duniya baki daya. Adadin kudi Euro miliyan dubu 750 da kasashen na EU suka ware domin wannan taimako ba'a taba samun irin sa ba a tarihin Euro, kamar yadda shugagban gwmanatin Jamus, Angela Merkel ta nunar ranar Litinin.

Shugaban gwamnatin ta Jamus, Angela Merkel a fili tayi magana game da abin da ta kira, halin matsi da aka shiga, wanda ba'a saba ganin irin sa ba, dake bukatarf mataki na musmaman da shima ba'a saba ganin irin sa ba daga kungiyar hadinkan Turai. Ministan harkokin wajen Sweden, Anders Borg har ma yace a ganin sa, kudin Euro, kamar dai wasu zakoki ne suka kewaye shi suna jira su cinye shi.

Yace a yanzu muna lura da fadi-tashi a kasuwnanin hada hadar kudi, amma a zahiri, kudin na Euro masu neman halaka shi ne suka yi masa kawanya. Idan har bamu dakatar da masu nean tauye kudin na Euro ba, to kuwa zasu haddasa rushewar kasashe masu amfani da wannan kudi, duk kuwa da ganin cewar da yawa daga cikin su su ke da laifin halin da auka shiga yanzu. Saboda haka ne yake da muhimmanci mu sami ci gaba, ba ma a game da daukar mataki na dogon lokaci ba, amma har da matakai na gajeren lokaci da zasu shafi hana samun mummunan gibi a kasafin kudin mu. Muna bukatar amsar da ta dace da wnanan matsala da ta taso cikin dare daya.

Amsar da shugabannin kasashe goma sha shidda da ministocinsu na kudi suka samar, lokacin taron kolin su a karshen mako kuwa ita ce: hadin kan na takardun kudi, kamar yadda yake a yarjejeniyar Maastricht ta shekara ta 1992 da yarjejeniyar Lisbon ta shekara ta 2009 ya zama tarihi. Matakin da kasashe masu amfani da kudin Euro suka dauka na taimakawa takwarorin su masu rauni da abin da ya kai Euro miliyan dubu 500, ya sanya wadannan kasashe suyi watsi da wata manufa mai matukar muhimanci, wanda a karkashin ta, wata kasa ba zata dauki lamuni na dimbin bashin dake kan wata kasar ba. Kwamishinan harkokin kudi na kungiyar hadin kan Turai, Olli Rehn yayi bayanin dalilin da ya sanya kasashen na Turai suka dauki matakin kaucewar bangaren yarjejeniyar Lisbon da ya hana taimakawa wata kasa ida ta fada dimbin bashi.

Yace wannan mataki babu shakka zai shafi manufofin kasashe masu amfani da kudin Euro, abin da zai kawo hadari ga tsarin gaba dayan sa. Wannan mataki ba shisshigi ne ga wata kasa daya mai amfani da kudin Euro ba, amma shisshigine ga yankin dake amfani da kudin Euro gaba daya da kuma kungiyar hadin kan Turai ita kanta. Saboda haka ne ya zama wajibi ayi amfani da aya ta 122 ta yarjejeniyar Lisbon, yadda za'a magance wannan hali mai matukar rikitarwa da aka shiga, wanda ma ya zarce yadda wata kasa guda zata iya maganin sa ita kadai.

A halin da ake ciki kuma, kasashe masu amfani da kudin na Euro sun fara daukar matakai na amincewa da gudumuwar su ga wannan shiri na hana fadi-tashin kudin a kasuwnanin duniya nan gaba. Majalisarf ministocin Jamus ta amince da gudummuwar da kasar zata bayar a tsarin da aka yi na tanadar da asusun da zai kasance dakudi Euro miliyan dubu 750 a cikinsa, wanda Jamus zata bayar da misalin Euro miliyan dubu 123 daga wannan adadi. Shugaban gwamnatin Jamujs, Angela Merkel tace sake samun raunin Euro kamar yadda aka fuskanta yanzu, zai haddasa mummunan hadari ga harkokin kudi na kasashen da abin ya shafa. A bayan Girka da ita ce ta haddasa raunin na Euro a yanzu, sauran kasashe da ake ganin sun kama hanyar shiga mummunan hali irin natga sun hada har Spain da Portugal da Italiya da Ireland.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Muh. Nasiru Awal