1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matan dake rike da mulki

February 25, 2010

Mata nawa ke riƙe da muƙamin shugaban ƙasa ko shugaban gwamnati a halin yanzu a duniya ?

https://p.dw.com/p/MAWE
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: AP
Tambaya daga Ibrahim Ibbo dake Kancari a ƙasar Burkina Faso, ya na so ne a gaya masa matan da suke riƙe da muƙamin shugaban ƙasa ko shugaban  gwamnati duniya  a halin yanzu. A yankin Latine Amurika, ƙasar Arjentina  Isabel Peron ta kasance mata ta farko  a wannan yankin da ta taɓa hawa karagar mulkin shugabacin ƙasa daga shekara ta 1974 zuwa 1976.Sai kuma Cristina Kirchner da aka zaɓa a shekara ta 2007 wadda yanzu haka ke riƙe da ragamar jagorancin ƙasar Arjentina. A ƙasar Chili akwai Michel Bachelet da aka zaɓa shugabar ƙasa a watan Janairu na shekara ta 2006,to saidai a halin yanzu ta zo ƙarshen wa´din mulkinta A ƙasar Philipines kuwa, Glorio Aroyo mataimakiyar shugaban ƙasa Joseph Estrada da aka hamɓarar da shi dalili da al´amuran cin hanci da karɓar rashawa ta maye gurbinsa a watan Janairi na shekara ta 2001, sannan a ka zaɓe ta a matsayin shugabar ƙasa mai cikkaken mulki a shekara ta 2004. Idan muka koma Indiya kuwa, Pratibha Patil ce ta taɓa zama mace shugaban ƙasa bayan ta lashe zaɓe a  watan Juli na shekara ta 2007. A nan nahiyar Turai an zaɓi Tarja Halonen a matsayin shugabar ƙasar Finlande a shekara ta 2000, sannan aka sake zaɓen ta karo na biyu a  watan Janairun shekara ta 2006. A Irlande,an zaɓi Mary Robinson a matsayin mace ta farko a kujerar shugaban ƙasa, kuma mace yar uwarta, wata takwararta mai suna Mary McAleese ta gaje ta an zaɓe ta a shekara 1997, aka kuma sake zaɓenta karo na biyu a shekara ta 2004. Sai a Lituaniya a ranar 18 ga watan Mayu na shekara ta 2009 aka zaɓi Dalia Grybauskaite. A ƙasar Swizland shugabar Doris Leuthard majalisar Tarayya ta dorawa yaunin jagoranxcinkasar daga shekara ta 2010, saidai cemma kamin ita akwai mata biyu da suka taɓa jagorancin wannan ƙasa.

A nahiyarmu ta Afrika kuwa, shugabar ƙasar Liberia ce Elen Searlef Johnson ta taɓa hawa wannan kujera mai alforma. An zaɓe ta a watan Nowemba na shekara ta 2005. Idan muka koma ɓangaren shugabanin gwamnati kuwa,a nan ƙasar Jamus Angela Merkel ta zama shugabar gwamnati ta farko tun daga watan Nowemba na shekara ta 2005. Sannan a ƙasar Island,Johanna Sigurdardottir ce ta taɓa hawan kujera shugabar gwamnati  a shekara ta 2009. A Krotiya Jadranka Kosor ita ce mace ta farko da ta hau muƙamin Firaminista shugabar gwamnati.Saki kuma  akasar Ukraine inda Iouliya Timoshenko ta hau wannan matsayi a shekarar 2005 da kuma 2007. A Bangladesh Cheick Hasina Wajed, tayi zama shugabar gwamnati daga 1996 zuwa 2001.Sannan ta sake hawa a watan Janairun shekara ta 2009. To saidai fa a halin da ake ciki yanzu duniya ta cenza, mata na cigaba da ƙara kutasawa ana damawa da su cikin harakokin siyasa.Idan ba a manta ba a ƙarshen shekara ta 2008, Hilary Clinton Sakatariyar harakokin wajen Amurika mai ci yanzu tayi hoɓasarmar tsayawa takarra shugabancin ƙasar Amurika.Haka zalika a ƙasar Faransa a zaɓen shugaban ƙasar da ya wakana shekaru ukku da suka gabata,saura ƙiris Segoléne Royal ta jam´iyar PS ta lashe zaɓen.

Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Abdullahi Tanko Bala