1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasan Afirka kashi 77 cikin 100

Claus Stäcker MNA
November 28, 2017

Matasan Afirka masu kwazo ne da hazaka ga su kuma da basira, amma kasancewa tsofaffi ne ke jan ragamar mulki a wannan nahiya, ba safai ake duba bukatun matasan ba da yawansu ya kai kashi 77 cikin 100 a nahiyar.

https://p.dw.com/p/2oOAw
Niger DW Hörer
Hoto: DW/A. M. Amadou

Kashi  77 cikin 100* na al'ummar Afirka Kudu da Hamadar Sahara matasa ne da ba su haura shekaru 35 ba. Suna zuwa makaranta, suna neman ilimi a jami'a suna kuma neman aiki. Suna son yin aure, suna son daukar nauyin kansu. Suna hulda da junansu a shafukan sada zumunta na Facebook da WhatsApp da Instagram. Sun gane cewa suna da rinjaye na kashi uku cikin hudu, amma ba a ba su damar tofa albarkacin bakinsu. Ba a mayar da hankali kan damuwarsu. ‘Yan siyasa ba sa daukar batunsu da wani muhimmanci.

Sau da yawa tsofaffi ne ke jan ragamar mulki. Robert Mugabe a Zimbabuwe yana da shekaru 93 kafin ya yi murabus. Ya kasa magance matsalolin matasan. Matasan Afirka masu kwazo ne da hazaka ga su kuma da basira, amma ba su da wata makoma ta a zo a gani. Shin ko ‘yan siyasa na ba da himma wajen duba  bukatunsu?

Dogon buri da hangen samun wata rayuwa mai kyau na ingiza matasa da yawa zuwa Turai ko Afirka ta Kudu ko wasu kasashen duniya, suna bin haramtattun hanyoyi masu hatsari don neman biyan bukata. A cikin shirye-shiryenta da muhawarori a shafukan sada zumunta, tashar DW tana tabo matsaloli da kuma fata na matasa. A muhawarori da ta gabatar a biranen Abidjan da Accra da Bamako da Banjul da Konakry da Dakar da Jos da kuma Yamai, DW tare da hadin gwiwa da tashoshin rediyo da ke hulda da ita sun tattauna da matasa da ‘yan siyasa a kan batun hijira karkashin taken ‘‘Hangen Dala…" Muhawarorin sun kasance masu zafi da sosa rai da kuma daure kai. Ya dai bayyana a fili bukatar tattaunawa da juna, a yi musayar ra‘ayi a kuma mika damuwar matasan ga wadanda alhaki ya rataya a wuyansu. Wannan shiri da a Turancin Ingilishi aka yi wa lakabi da ‘‘The 77percent" wato ‘‘Matasan Afirka kashi 77 ne" zai kasance wani babban dandali na musayar ra'ayoyi a shafukan sada zumunta da rediyo da kuma telebijin.

Stäcker Claus Kommentarbild App
Claus Stäcker- shugaban sashen Afirka na DW

Shirin na Matasan Afirka kashi 77 ne zai labarta ya taimaka ya kuma nishadantar da ku. Matasa da kansu ne za su tsara abubuwan da ya kunsa. Ko dai ba da shawarar neman aiki ko sana'ar kanku ko muhimman shawarwari daga kasashe dabam-dabam ko tambayoyi masu tsauri ga ‘yan siyasa. Za mu gabatar da hotuna na barkwanci - wato dandalin Matasan Afirka kashi 77 ne zai ba da damar yin nishadi da raha da fatan cimma burin abin da kuke sha'awar zama a gaba. Dandali ne na rukunin wadanda suka fi rinjaye a Afirka.

Jama'a da dama sun san DW a matsayin tashar rediyo. Da yawa daga cikin kakanni maza da mata sun taba sauraron shirye-shiryen Deutsche Welle. Kusan 'yan Afirka miliyan 40 ke kama tashar DW a kowane mako. Fiye da miliyan 4 na bin DW a Facebook. Manufar kafa tashar ba ta canja ba. Muna sauraron kowane bangare na al'umma, muna kuma ba da rahotanni bisa gaskiya da adalci. Matasan Afirka kashi 77 dandali ne da za mu saurari wadanda suka fi rinjaye a Afirka. Zai kuma kasance muryarsu.

Da Ingilishi shirin na da alamar #The77percent

Da Hausa yana da alamar #MatasanAfirkakashi77ne

Ku biyo mu don zama wani bangare na shirin.

 

*Bayani daga Bankin Duniya