1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasan Niger Delta sun ƙara yin garkuwa da ma´aikatan haƙo man Petur

October 10, 2006
https://p.dw.com/p/BugJ

A yankin Niger Delta mai arzikin man petur, da ke kudancin Nigeria, matasa masu fafatakar ƙwato yancin yankin, sun ,kara garkuwa, da wasu ma´aikatan kampanin haƙƙo pan petur na Shell.

Sanarwar da hukumomin kampanin su ka hiddo, ta rataya alhakin wannan aika-aika, ga matasan ƙabilar Oporoma, a jihar Bayelsa.

Sanarwar ta Shell ta ƙara da cewa, ya zuwa babu wanda ya samu rauni, daga cikin ma´aikatan ta, da haɗarin ya rutsa da su, sannan hukumomin jihar, sun aika tawaga ta mussamman, domin tantanawa da shugabanin matasan.

A halin an rufe rijiyoyi da bututun mai na yankin da al´amarin ya wakana,hakan zai hadasa assara ganga 12.000 a ko wace rana.

A tsukin wattani 9 da su ka gabata an rufe riyiyoyi da dama a Niger Delta, a sakamakon tashe-tashen hankulla.

A satin da ya wuce, matasan sun kai irin wannan hari, a jihar Rivers, inda su ka kashe sojoji 14 na Nigeria, tare da yin awan gaba, da ma´aikatan mai 25, wanda har yanzu, babu ɗuriyar 7 daga cikin su.