1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

matashi ya kirkiro na'urar auna gina

June 13, 2017

Wani matashin malamin kwaleji a Najeriya ya kirkiro na'urar auna inganci gine-gine.

https://p.dw.com/p/2ecgC
Nigeria Gobarau-Minarett Katsina
Hoto: DW

A Jihar Katsina da ke Najeriya wani malami a tsangayar fasahar gine-gine a kwalejin kimiyya da fasaha na tunawa da Janar Hassan Usman Katsina, ya kirkiro na'urar auna ingancin gini a lokaci guda musamman gini wanda ya kunshi kankare, sabanin baya dole sai gini ya kai kwana 28 sannan a gane ingancin.

Kirkiro wannan na'ura dai ya sa malamin ya zo na biyu a wani bajakoli na fasaha da aka yi a Abuja, inda masana harkar gine-gine suka bayyana cewa na'urar ita kadaice irinta a duniya,

Wannan na'ura dai ana amfani da ita a kowane gini kuma kirkiro na'urar nada nasaba da yadda gine-gine ke yawan rushewa saboda rashin sanin hakikacin ingancinsa kamar yadda wanda ya kirkiro na'urar Injiniya Sama'ila Bawa Faskari. A kasashen Afirka masu tasowa akwai hazikan mutane masu dinbun basira sai dai basirar kan disashe saboda ba sa samun gwarin gwiwa daga mahukunta.