1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar Aids a Jamus

August 26, 2004

Kimanin Mutane dubu arba'in da uku ke dauke da kwayar HIV a nan Jamus, kuma cutar Aids sai dada yaduwa take yi musamman tsakanin matasa na kasar sakamakon sako-sako da suke yi da ita.

https://p.dw.com/p/Bvh0
Ministar lafiya ta Jamus Ulla Schmidt
Ministar lafiya ta Jamus Ulla SchmidtHoto: AP

Bisa ga ra’ayin ministar lafiya ta Jamus Ulla Schmidt mai kamata a yi sako-sako da matakan riga kafin cutar Aids dake dada yaduwa a sassa dabam-dabam na duniya ba. Tuni mutane suka manta da gaskiyar cewa cutar mai karya garkuwar jikin dan-Adam ba ta da magani, kuma tana yaduwa a cikin hamzari, musamman a kasashen gabacin Turai. Wannan shiyyar ta fi kowace fama da yaduwar cutar a cikin gaggawa, fiye ma da nahiyar Afurka yanzu haka. Hatta a nan Jamus, kusan kullu-yaumin, sai an samu karin masu kamuwa da kwayoyinta. A saboda haka bai kamata a rika yi wa matsalar rikon sakainar kashi ba. Wajibi ne a rika janyo hankalin jama’a domin su ankara da ita a cewar ministar lafiya ta Jamus Ulla Schmidt, wacce ta kara da cewar:

Tun bayan billar cutar Aids misalin shekaru 20 da suka wuce ta halaka mutane kimanin miliyan 22. Za a iya fahimtar barazanar dake tattare da ita ta la’akari da gaskiyar cewa a halin yanzu haka mutane miliyan 40 ke dauke da kwayoyinta kuma akan samu masu sabbin masu kamuwa da ita bayan kowadanne mintuna 10 a sassa daban-daban na duniya.

A nan Jamus dai mutane dubu 43 ke dauke da kwayar HIV kuma wasu dubu biyar daga cikinsu na fama da cutar Aids. Matsalar ta fi addabar matasa, wadanda basu da wata cikakkiyar masaniya a game da barazanar wannan cuta. Wani binciken da aka gudanar ya nuna cewar kimanin kashi 16% na matasa na tattare da imanin cewar da zarar mutum ya kamu da cutar Aids za a fara ganin alamomin cutar sun bayyana a jikinsa. Wannan ragon azanci ya taimaka aka samu karuwar yawan matasan dake kamuwa da kwayar HIV. Kimanin kashi 23% daga cikinsu kuwa ba su cimma shekaru 25 da haifuwa ba. Rikon sakainar kashin da ake wa cutar ta Aids abu ne da zai jefa matasan cikin mawuyacin hali game da makomar rayuwarsu nan gaba, in ji wani da ake kira Bernhard Bieniek, mai magana da yawun kungiyar yaki da yaduwar kwayar HIV a Jamus. Wajibi ne a tashi tsaye wajen wayar da kan matasa, musamman ma a gabacin kasar, inda ake dada samun karuwar yawan masu kamuwa da kwayar HIV. Babban dalilin haka kuwa shi ne rashin gabatar da wani takamaiman mataki na wayar da kan jama’a game da cutar a tsofuwar Jamus ta Gabas a cikin shekarun 1980. Daya rukunin dake fuskantar barazana kuma shi ne bangaren baki ‚yan kaka-gida kuma wajibi ne a dauki nagartattun matakai na wayar da su game da matakan riga kafin cutar ta Aids. Wadannan matakai na wayarwa, kamar yadda ministar lafiya ta Jamus ta nunar, sune ya kamata a ba su fifiko wajen yaki da yaduwar Aids kuma a saboda haka gwamnati ta ware tsabar kudi Euro miliyan tara domin gudanar da wannan mataki na kamfe, kuma ba zata yi tsumulmular ko da sisin kwabo akan wannan manufa ba.