1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar Ambaliya a kudancin Asia

August 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuEV

Miliyoyin mutanen da balain ambaliyan ruwa ya tilastasu ficewa daga gidajensu, a sassa daban daban na yankin kudancin Asia ,na bukatar agajin gaggawa na abinci da rzuzwan sha ,ayayinda jamian agaji da sojoji ke cigaba da kokarin kai musu dauki.

Ambaliyar wadda aka bayyana da kasancewa mafi muni daya addabi wannan yankin a shekareu da dama da suka gabata,ya ritsa da kimanin mutane milion 31,ayayinda sama mutane 1,600 suka rasa rayukansu, akasashen India da Bangladash da Nepal ,ambaliyar da aka dangana da damuna mai karfi daya sauka a yankin daga watan yuni.

Jihar Bihar dake kasar dai,itace Ambalin yafi rfitsa da ita.Shugaban Hukumar agajin Balau daga indallahi na jihar Manoj Srivastava ,ya bayyana cewa sama da kauyuka dubu 6 ne ambaliyar ta wanke,sai dai ruwan saman ya fara daukewa.