1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar ambaliyar ruwa a Jamus

April 3, 2006

A wasu yankuna na kasar Jamus ana fuskantar ambaliyar ruwa koguna

https://p.dw.com/p/Bu0u
Ambaliyar ruwa a Dresden
Ambaliyar ruwa a DresdenHoto: AP

Mutane da dama sun shiga hali na rudu da rashin sanin tabbas, musamman a yankin Riesa, wanda ya taba fuskantar mummunar almabiyar ruwa a shekara ta 2002. An saurara daga daya daga cikin wadanda matsalar ambaliyar ruwan ta shafa yana mai bayanin cewar:

A yanzun dai babu wata mafita daga wannan masifa. Dukkan wadanda suka yi bakin kokarinsu wajen gyara bannar da ambaliyar tayi musu a shekara ta 2002, a wannan karon tilas su saduda. Bana jin cewar masu lambun zasu ci gaba da wannan harka a karo na biyu.

Amma a hakika har yau akwai mutanen da ba su fid da kauna ba suna masu gwagwarmayar dakatar da ruwan dake malala zuwa gidajensu. Tuni rudunar sojan Jamus ta gabatar da wani mataki na jigilar mazauna yankin na Riesa, saboda motoci ba sa iya amfani da titunan yankin, kamar yadda aka ji daga bakin laftana-kanar Stefan, wanda yake cewar:

A hakika ruwan bai kai intaha ba ta yadda zai hana zirga-zirgar manyan motoci. Amma da zarar zurfin ruwan ya kai tsawon mita daya da digo 20 to wajibi ne mu dakatar da zirga-zirgar motocin saboda kare lafiyar jama’a.

A can birnin Dresden dake bikin samun shekaru 800 da kafuwa kuwa tuni mahukunta suka umarci wasu mutane dari da su bar gidajensu, a baya ga wadanda suka tashi daga gidajen nasu bisa radin kansu. An ji daga bakin wani daya daga cikin mazauna yankin Laugebast-Zschieren dake garin na Dresden yana mai fadin cewar:

Babu wani dalili na nuna taurin kai. A halin yanzu haka ba mu da wuta kuma ruwan ba ya da makwarara, a saboda haka muka tattara abin da zamu iya dauka muka fice daga gidanmu.

A wani sabon ci gaba dai rahotanni sun ce an fara samun saukin lamarin a jihar Bavariya, in banda wasu yankuna dake fama da ambaliyar jefi-jefi, saboda ruwan kogin Donau ya dan ja da baya zuwa zurfin mita 7 da digo 63. Kuma a halin yanzu ba a sa ran cewar lamarin zai yi tsamari a wannan yanki.