1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira na ci gaba da isa Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afarSeptember 5, 2015

Hukumar kula 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yaba wa kasashen Ostiriya da Jamus bisa yanke shawara bai wa 'yan gudun hijira damar tsallakakan iyakokinsu.

https://p.dw.com/p/1GRd6
Daruruwan 'yan gudun hijira sun isa birnin Munich
Hoto: Reuters/L. Barth

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanara da ta fitar inda ta ce lallai gwamnatocin kasashen biyu sun nuna cewa suna da jin kai da tausayi. Hukumar da ke da shalkwata a birnin Geneva ta kuma yabawa kungiyoyin fararen hula da kuma al'ummar kasashen na Jamus da Ostiriya sakamakon maraba da kuma taimakon da suke bai wa 'yan gudun hijirar wadanda dama ke matukar bukatar taimakon, wanda ta bayyana shi da cewa babban abin yabawa ne daga al'ummomin kasashen biyu. Hukumar ta kara da cewa matakin kasashen biyu ya tilastawa sauran gwamnatocin kasashen nahiyayr ta Turai fara sauya ra'ayin da suke da shi a kan 'yan gudun hijira. A hannu guda kuma wasu daruruwan 'yan gudun hijirar sun isa tashar jiragen kasa ta birnin Munich na Jamus daga kasar Hangari.