1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar cin hanci a Afghanistan

November 25, 2009

Ƙasar Afghanistan ce a sahun farko a matsalar cin hanci da rashawa a duniya kamar yadda Transparency International ta nunar

https://p.dw.com/p/Kg7h
Shugaba Karzai na shirin gabatar da sabuwar gwamnati a yayinda ake fama da cin hanci a AfghanistanHoto: picture alliance / dpa

A yayin da shugaba Hamid Karzai na ƙasar Afghanistan ke shirye shiryen sanar da sabuwar majalisar ministocin gwamnatinsa, hukumomin ƙasar sun bayyana cewar, nan ba da daɗewa ba ne zasu shirya wani babban taron tattauna batun matsalar cin hanci da rashawar da ya yiwa ƙasar katutu.

Hukumomi a ƙasar Afghanistan, sun sanar da cewar, zasu gudanar da babban taron da zai taɓo matsalar cin hancin da ƙasashen yammacin duniya ke ƙara yin matsin lamba ga gwamnatin shugaba Hamid Karzai na ƙasar daya ɗauki matakan kawo ƙarshenta.

Mai magana da yawun shugaba Karzai, Humayun Hamidzada, ya ce babban taron, zai kuma taɓo batun sake gina ƙasar game da bunƙasata, tare da haɗin gwiwar masu baiwa ƙasar agaji.

Wannan sanarwar dai, ta zone jim kaɗan bayan da masu gabatar da ƙara a ƙasar, suka bayyana cewar, suna binciken wasu manyan jami'an gwamnati da 'yan siyasa 15 bisa zargin cin hanci da rashawa. Daga cikin waɗanda ake binciken, har da ministoci uku dake cikin gwamnatin shugaba Hamid Karzai, da kuma wasu tsoffin ministoci 12, ko da shi ke kuma ba'a kai ga bayar da sammaci ba.

Shugaba Hamid Karzai dai ya yi alƙawarin cewar, dukkan waɗanda ake zargi da cin hanci a wa'adin shugabancinsa na farko, zasu fuskanci shari'a.

Symbolbild Korruptionsindex Transparency International Jahresbericht Wirtschaftskorruption p178
Shugaba Karzai yayi alƙawarin yaƙar cin hanci a ƙasarsaHoto: dpa

Robert Bailey na ƙungiyar agaji ta OXFAM dake da tushe a ƙasar Ingila, ƙungiyar da kuma ta fitar da rahoton dake nuna irin yadda cin hanci ya yi katutu a Afghanistan ya ce, ƙasashen duniya zasu gamsu ne kawai, idan har suka ga cewar, da gaske gwamnatin take yi:

"Idan har mun ga ana ɗaukar mataki a ƙololuwar gwamnati, ko dai a ɓangaren shari'a, ko rundunar soja, ko kuma sauran ma'aikatun gwamnati, da kuma a tsakanin 'yan siyasa. Idan har muka ga ana ɗaukar tsauraran matakai a irin waɗannan wuraren, to, kuwa hakan zai ƙarfafa gwiwar nagartattun mutanen dake cikin gwamnati da ma su kansu al'ummar Afghanistan, waɗanda ke ƙaunar ganin ana sarrafa kuɗaɗen ƙasar cikin gaskiya da adalci, domin amfanar jama'ar ƙasa baki ɗaya."

OXFAM Logo
Oxfam ta ce cin hanci na hana ruwa gudu wajen raya makomar AfghanistanHoto: AP Graphics

Jiya talata ce kuma, shugaba Hamid Karzai ya ce, nan da makonni biyu ne zai sanar da sabuwar majalisar ministocinsa, a dai-dai lokacin da ƙungiyar Transparency International dake yaƙi da cin hanci a duniya ta sanya ƙasar cikin jerin ƙasashen dake sahun farko wajen fuskantar matsalar a duniya baki ɗaya. Pascal Fabie, darektan kula da yankin Asiya a ƙungiyar, ya ce, shigar da al'umma cikin sha'anin mulki ne kawai zai taimaka wajen kawo ƙarshen rashawa a Afghanistan:

"Muna buƙatar shigar da jama'a cikin harkokin gudanarwa a wurin da sha'anin tsaro ya taɓarɓare, tsarin ma kansa na tattare da ɗimbin matsalar cin hanci da rashawa . Mutane na fargabar ɗaukar fansa akansu , saboda haka ba zasu iya tsayawa kai da fata ba wajen yaƙi da matsalar cin hanci, tunda tuni suke fafutukar tafiyar da rayuwarsu. Mutane zasu shiga a dama dasu ne kawai - idan har sun ga cewar, da gaske ne gwamnatin take wajen yaƙi da rashawar."

A mako mai zuwa ne, shugaba Obama na Amirka zai sanar da sabbin matakan sojin da zai ɗauka a ƙasar ta Afghanistan, a yaƙin da ƙasarsa ke yi da ƙungiyar Taliban.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Ahmad Tijani Lawal