1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar Farin Dango A Afrika

September 1, 2004

Rahotanni masu nasaba da kungiyar abinci ta FAO sun ce kasashe da dama na yankin Sahel na fuskantar barazana ga makomar amfanin nomansu sakamakon yaduwar farin dango

https://p.dw.com/p/Bvgq

A lokacin da yake bayani wani jami’in kungiyar abinci da noma ta MDD da ake kira Clive Eliott ya ce matsalar farin dangon tafi yin tsamari ne a kasar Mauritaniya, inda suka bannatar da filayen noma dake da fadin kadada miliyan daya da dubu 600. Jami’in ya kara da bayani yana mai cewar:

Wadannan kwari suna ciyar da kansu daga hatsi, kuma a daidai yanzu ne aka fara noma, wato amfanin gonakin ba su fara girma ba, ballantana a kiyasce yawan barnar da farin suka yi.

Amma lamarin zai zama akasin haka idan tsire-tsiren suka fara girma kuma aka sake fuskantar wata sabuwar rundunar ta farin dango nan da makonni biyu masu zuwa. Domin kuwa farin su kan ribanya har ninki ashirin a lokaci guda kuma lamarin ba kawai ya takaita ne a kasar Mauritaniya ba, suma kasashen Mali da Nijer da Senegal da wasu yankuna na Chadi da Burkina Faso na fama da matsalar ta farin dango, kuma mai yiwuwa abin ya rutsa da Nijeriya. Kowace runduna ta farin dangon ta kunshi fari kimanin miliyan tamanin dake da ikon tafiyar kilomita 130 a rana idan an samu kyawon yanayi tare da mummunar barna. Matsalar farin dangon shi ne kasancewar lokaci-lokaci ne su kan billa, inda a karo na karshe da aka fuskanci annobarsu ya kama shekaru 15 da suka wuce. Wannan shi ne ya sanya ba kasafai ba ne ake ba da la’akari da matsalar ba. Kasashen Maroko da Aljeriya sun kashi abin da ya kai dalar Amurka miliyan 80 domin riga kafin annobar, amma kasashen dake bukatar taimako ruwa a jallo a yanzun sune na yankin Sahel. Wajibi ne a gabatar musu da taimakon da zai kai dalar Amurka miliyan 100. Kawo yanzun kuwa duka-duka yawan abin da aka bayar na taimako bai wuce dala miliyan talatin da ‚yan kai ba. Ita ma Jamus tana daridari wajen ba da taimako saboda adawa daga jam’iyyar the Greens mai ra’ayin kare kewayen dan-Adam. Amma fa tilas ne a yi amfani da maganin kashe kwari muddin ana fatan a shawo kan matsalar. Wani abin da aka kasa ba da la’akari da shi shi ne gaskiyar cewar manoman da lamarin ya shafa ba zasu yi wata-wata ba wajen yin kaura zuwa manyan garuruwa da birane domin dogaro akan taimakon abinci. A sakamakon sako-sako da aka rika yi da matsalar a yanzun ba za a iya dakatar da yaduwar farin ba, illa kawai a yi bakin kokari wajen kare makomar wasu daidaikun filayen noma. Kuma idan farin suka yadu zuwa kasar Sudan to lamarin sai kuma gyaran Allah.