1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar karancin abinci a Malawi ta yi muni

Mohammad Nasiru AwalMay 25, 2016

Sama da rabin 'yan kasar Malawi na bukatar taimakon abinci daga ketare saboda fari da kasar ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/1IuS5
Simbabwe Dürre Maisfeld
Hoto: picture alliance/Photoshot

Gwamnatin kasar Malawi ta ce sama da rabin al'ummar kasar su kimanin miliyan 16 ke bukatar taimakon abinci sakamakon wani fari mai tsanani. Ministan noma na kasar George Chaponda ya fada wa kamfanin dillancin labarun Jamus na DPA cewa kimanin mutane miliyan 8.5 a kasar da ke a yankin kudancin Afirka za su fuskanci karancin abinci saboda rashin saukar ruwan sama sakamakon sauyin yanayin nan na El Nino. Ministan ya ce yanayin da ya janyo wani zafi mai tsanani ya haddasa karancin albarkatun gona. Tun a ranar 12 ga watan Afrilu shugaban kasa Peter Mutharika ya ce wani bala'i ya afka wa kasar sannan ya nemi taimakon abinci daga kasashen duniya.