1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar karancin abinci a matsayin hakin dan Adam

Mohammad Nasiru AwalOctober 16, 2006

An kiyasce cewar mutane sama da miliyan dari takwas a ko-ina cikin duniya ba sa samu abin sakawa bakin salati.

https://p.dw.com/p/BvTE
Karancin abinci a Afirka
Karancin abinci a AfirkaHoto: AP

A halin da ake ciki mutane kimanin miliyan 850 a ko-ina cikin duniya ke fama da karancin abinci. Wani kiyasin da kungiyar abinci da aikin noma ta MDD FAO ta yi ya yi nuni da cewa a shekara ta 2010 yawan masu fama da karancin abinci zai kai miliyan 680. Duk da cewa duniya na samar da kayan abinci da zai isa a ciyar da kowa da kowa, amma rashin raba daidai ke kawo cikas a kokarin da ake yi na kawad da yunwa a doron kasa. Kamar kullum dai a rubuce ana cimma burin da aka sanya a gaba, amma a aikace ba haka abin yake ba. ´Yancin samun abinci na matsayin doka a kundin tsarin mulki na kasashe 22 na wannan duniya ta mu. To amma babu wani mataki na tabbatar da wannan ´yanci, inji kungiyoyi kare hakkin dan Adam. Ana Maria Franco wakiliyar kungiyar samar da abinci da bayanai FIAN, a Colombia ta ce duk da cewa doka ta ba da damar yin karar ´yan siyasa in ma ta kama a daure su a kurkuku idan suka keta hakkin bil Adama, amma daidai da sau daya ba´a taba yin haka idan aka take hakin mutum na samun abin sakawa bakin salati.

“Akan shigar da kararraki akan wasu batutuwan, alkalai ma kan tabo batun hakin samun abincin, amma ba´a taba gurfanad da wani da aikata wannan laifi ba. Saboda haka yanzu muna cikin aikin kirkiro da wasu dubaru kuma muna fata hakan mu zai cimma ruwa.”

Ba a Colombia ce kadai hakan ke faruwa ba, a wasu kasashe ma akan yi batu game da hakkin ma´aikata da jin dadin jama´a amma ba mai kula da batun samar da abinci a matsayin hakin dan Adam. Rashin wani katabus daga shugabanni da kuma jahilcin jama´a kan abin da aka sanya a gaba shi ke hana ruwa gudu bisa manufa, inji Franco.

Hakin dan Adan na samun abinci ba ya tsaya kadai akan ba da taimakon kayan abinci na gaggawa ba. Manufa ita ce samar da hanyoyin ciyar da kai da kai wato kamar samar da filayen noma da basussuka ga kananan manoma. ´Yan siyasa da wadanda abin ya shafa a kasashe matalauta ba su fahimci abin da ake nufi da hakkin samun abinci ba. Da yawa daga cikin su na daukar matsalar yunwa da talauci tamkar wani bala´i daga Inadallahi, saboda haka ba sa damuwa da kai kara.

To amma hakan ka iya canzawa a kasar Brazil, inda mutane kimanin miliyan 64 ke rayuwa karkashin wani tsari na samar da abinci cikin gaggawa. A halin da ake ciki an kafa wata hukuma karkashin Flavio Valente don duba batutuwan da suka shafi hakkin samar da ruwa da kasa da abinci tare da bawa gwamnati shawarwari, in kuma hali ya kama ta tuntubi MDD.

“Kawo yanzu mun samu ci-gaba na a zo a gani. Mun shawo kan gwamnati tana zama kan teburin shawarwari da kananan hukumomi da kungiyoyi a kauyuka don gano bakin zaren warware matsalolin da ke a kasa. Ko da yake ba´a kai gaci ba, amma yanzu kungiyoyi sun waye kuma sun samu karfin guiwar kare hakin su.”

Wata kasa guda daya dai ba zata iya magance wannan matsala ita kadai ba, dole sai gamaiyar kasa da kasa ta kara matsa kaimi don tabbatar da hakin na samun abin sakawa bakin salati ga kiowa da kowa.