1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar rashin aikin yi a Jamus

March 16, 2005

Da yawa daga ma'aikatan da suka yi asarar guraben ayyukansu ke fama da rashin koshin lafiya sakamakon karayar zuciya

https://p.dw.com/p/Bvcj

Wani bincike da masana suka gudanar ya gano cewar akwai banbanci tsakanin maza da mata da kuma tsakanin ‚yan gabaci da ‚yan yammacin Jamus dangane da yadda kowane daga cikinsu ke tallafar matsalar ta rashin aikin yi. Bayanai sun nuna cewar mazauna yankin gabacin Jamus sune suka fi jin radadin matsalar ta rashin aikin yi dake tasiri ga lafiyarsu. A yammacin kasar kuwa lamarin ya fi shfar maza. Su kansu manazartan da suka gudanar da wannan bincike sai da suka yi mamakin wannan sakamako. Kimanin kashi 20% na marasa aikin yin da aka nemi jin albarkacin bakinsu sun nuna cewar suna fama da radadi ta yadda basu da ikon tabuka kome a harkokin rayuwa ta yau da kullum. Wannan maganar ta shafi kashi daya bisa uku a yammaci da kuma kashi daya bisa bakwai a gabacin Jamus, duk kuwa da cewar wannan yankin ya fi fama da yawan marasa aikin yi. A zamanin baya, a karkashin tutar tsofuwar Jamus ta Gabas, gwamnati ce ke kula da makomar rayuwar jama’a. Ita ce ke ba wa mutane aiki. Har yau kuwa akwai wannan akida tattare a zukatan mutane, na cewar gwamnati ce ke da alhakin samar musu da guraben aiki. Wani abin lura kuma shi ne kasancewar ba a mayar da marasa aikin yin saniyar ware a harkokin rayuwa ta yau da kullum ba, saboda matsalar ta rutsa da kowane bangare na jama’a a yankin na gabacin Jamus, bisa sabanin yadda lamarin yake a yammacin kasar, inda mutane ke da akidar cewar duk mai son aiki zai iya samu, illa dai makiwata kawai. Dangane da matsayin lafiyar marasa aikin yin kuwa an kiyasce cewar kashi daya bisa uku na maza da kuma kashi daya bisa hudu na matan da basu da aikin yi a yammacin Jamus suna fama da rashin lafiya. Dalilin haka kuwa shi ne karayar zuci da kan rutsa da mazan ta yadda suke ganin cewar ba su da sauran alfanu a rayuwarsu. Maza dai bisa al’ada sune ke da alhakin ci da iyali a sakamakon haka duk namijin da yayi asarar aikinsa sai ya rika ji kamar takaici zai kashe shi, lamarin dake tasiri ga makomar lafiyarsa. A dai halin da ake ciki yanzun masana na ci gaba da binciken hanyoyin da zasu taimaka a dakatar da wannan mummunan ci gaba, misali tayi wa marasa aikin yin tayin shiga a rika damawa dasu a ayyuka na sa kai, kamar taimakon gajiyayyu da marasa galihu. To sai dai kuma a inda take kasa tana dabo shi ne wadannan ayyuka na sa kai ne kawai babu wata lada ta albashin da za a ba wa mutum.