1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar ruwan sha a Amirka

Melanie Cura Dabal
December 12, 2017

Samun wadataccen ruwa na zama babban kalubale ga miliyoyin al'ummar da ke zama birnin Detroit na kasar Amirka inda ake katse layin ruwa ga daruruwan gidaje da basu iya biyan kudin ruwa ba.

https://p.dw.com/p/2pExp
Bildergalerie Detroit USA Neues Leben nach der Insolvenz
Masu zanga-zanga kan karancin ruwa a AmirkaHoto: Getty Images/Joshua Lott

Valerie Jean Blakely wata uwa mai yara biyar ta bayyana irin yadda ta kaya tsakanin ta jami'an da ke lura da samar da ruwa da suka zawo gidanta dan katse hanyar dake shigar da ruwa gidanta sabida rashi biyan kudin ruwa, abun da ta turje da cewar ba zai yuwu ba ta na mai shaida musu cewa sai dai su kira yan sanda domin tana da yaya da take wa girki wani hali ake so ta fada ciki.

Bayan jam'an sun tafi ne Valerie ta gano cewa duk makwabtan basu yi sa'a ba, don an katse hanyoyin da ke samar musu ruwa. Bayan ma'aikatan sun yi burus da koke da wata dattijuwa yar shekaru 86 ta yi, inda suka datse layin ruwan gidanta, Valerie Jean Blakely ta yi rubutu a shafin ta na facebook, abun da ya sa mutane daga wurare da dama jibge ruwa galan dari a gidanta, sai dai tana tunanin makwabtan ta da ke zama babu ruwan, kamar yadda ta ce.

"In ka lura da yadda ko kadan ba daraja makwabtan ka, kuma kowa ya yi shuru, ai daya yake ace ana cikin wani yanayi na yaki''

Haka dai wadannan al-ummomi ke rayuwa babu ruwa inda wasu suka shafe shekaru uku cikin wannan yanayi, duk da cewa birnin na Detriot na tsakiyar wasu koguna ne guda biyu,

Tun shekara ta 2010, kudin ruwa ke ci gaba da tashi abun da ke jefa marasa galihu a birnin cikin wani hali na ha'ula'i, inda daga shekara ta 2004 zuwa yanzu gidaje dubu dari ne ke zaune babu ruwa, sakamakon gaza biyan kudin ruwan da suka yi.
  
A cewar  Peter Hammer farfesa a fannin ilimin sharia  da ke jami'ar Wayne a birnin na Detroit, wannan lamarin babbaar matsala ce da bai dace ace ana samun ta cikin al'ummomin da ake ganin sun cigaba.

USA Trinkwasser in der Stadt Flint vergiftet
Tankin tace ruwan sha a MichiganHoto: Reuters/R. Cook

"Ban ga dalilin da zai sanya duk wata al-umma da ta cigaba za ta dinga rufe hanyoyin samar da ruwa ga al-umma ba, wadanda da yawa daga cikin yara kanana ne marasa lafiya, don haka akwai bukatar tashi don magance wannan matsala ta ruwa". 

Valerie Jean Blakely da ke da yara a birnin na Detriot, ta bayyana cewa maimakon magance matsalar, hukumomi ma bita da kulli suke wa iyaye mata.

'' Indai kina zaune ke kadai ne da yaranki kuma makarantar yaran ta gano cewa gidanku babu ruwa, to za su sanar da ma'aikatar da ke kula da yara inda su kuma za su karben yaran daga hanun iyayen"

Tun daga ranar da hukumomin suka yi yunkurin katse layin ruwan gidan Valerie Jean Blakely da hadin gwiwar wasu kungiyoyin 'yan fafutika sun fara wani kamfe na samar da sabon tsari ta yadda za'a dinga cajin kudin ruwa daidai da karfin arzikin al-umma.

Birnin na Detriot dai ba shi kadai ke fuskantar irin wannan matsala ba, wani rahoto da jami'ar jihar Michigan ta kasar Amirka ta fitar, ya yi nuni da cewa izuwa shekar ta 2020, kashi daya cikin uku na gidajen Amirkakawa maza su iya biyan kudin ruwa ba muddin kudin na ruwan ya cigaba da tashi.

Ko da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana irin matsalar ruwan da ake fama da ita a birnin na Detroit, a matsayin wata babbar masifa da ke fuskantar al-umma kuma wani yana na take hakin jama'a.