1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar ruwan sha a birnin Ouagadougou

Salissou BoukariMay 1, 2016

Ofishin ministan ruwa na kasar Burkina Faso ya sanar da daukar sabbin matakan sassauta matsalar ruwan sha da ake fuskanta a Ouagadougou babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/1Ig1E
Südafrika Dürre Wasserverteilung
Hoto: picture-alliances/dpa//K. Ludbrock

Cikin wani jawabi ne dai da ya yi da yammacin ranar Asabar, Ministan ruwa da kula da tsafta Niouga Ambroise Ouedraogo, ya sanar cewa sabon matakin zai fara aiki ne daga ranar Talata mai zuwa, inda za a fara bai wa wani bangare na birnin ruwan na tsawon awoyi 12, kafin daga bisani a yanke a bai wa dayan bangaran.

Wata mata mai iyali ta sanar wa manema labarai cewa, tana tashi ne tun daga karfe daya na dare tare da 'ya'yanta ta tsura wa fanfo idanu ko zai kawo ruwa, kuma ta ce sai su kai har karfe biyar ba tare da ruwan sun zo ba. A kowane lokaci dai a birnin na Ouagadougou ana ganin jerin bidoduwa na masu neman ruwa a bakin Fonfuna, inda wasu unguwannin ke shafe kwanaki uku zuwa biyar ba tare da sun samu ruwan ba.

Matsalar ruwa dai ta fara ne tun daga shekara ta 2013, kuma ta karu a wannan lokaci sakamakon mugun zafin da ake yi na maki 40 zuwa 45 a ma'aunin Celsius.