1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar shara a Italiya

Halimatu AbbasJanuary 7, 2008
https://p.dw.com/p/Clb7

A ƙasar Italiya an yi kira ga sojoji da su taimaka wajen kawar da shara dake maƙe a birnin Napples dake kuddacin ƙasar. Mazauna wata unguwa a wannan birni sun ƙange hanyoyi domin nuna adawarsa da sake buɗe wani ramin zud da shara da aka rufe shekaru goma sha ɗaya da su ka gabata sabo da kare lafiyar al’uma.Prime ministan ƙasar Romano Prodi ya ba da umarnin sake buɗe makarantu duk da tsoron da aka bayyana cewa sharan ka iya haifar da ɓarkewar cuta.A yau ne yake ganawa da majalisar ministocinsa don shawarta wannan matsala. Wannan rikici ya kunne kai ne makonni biyu da suka gabata bayan da motocin kwasan shara suka daina aiki sakamakon cikan wurare zud da shara. Hukumar zantaswa ta Ƙugiyar Tarayyar Turai ta ce za ta gurfanad da Italiya a gaban sharia a dangane da gazawarta wajen cimma dokokin ƙungiyar na kawar da shara ba tare da yin illa ga lafiyar alumma da mahalli ba.