1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar soke hukuncin kisa daga tsarin dokokin kasashe na duniya baki daya.

YAHAYA AHMEDOctober 10, 2005

Ran 10 ga watan Oktoba ne, ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kayyade tamkar ranar yaki da hukuncin kisa. Bisa wasu alkaluman da kungiyar fafutukar kare hakkin dan Adam a duniya, wato Amnesty International ta buga dai, a shekarar bara, an sami karin yawan hukuncin kisan da aka zartar a duniya, fiye da na shekaru 25 da suka wuce.

https://p.dw.com/p/BvZ1
Alamar Amnesty International.
Alamar Amnesty International.

Bisa ra’ayin al’umman yankin nahiyar Turai dai, ko wane mahaluki na da `yancin rayuwa har cikar ajalinsa. Mai laifin kisan kai ma na da wannan hakkin, wanda kuma bai kamata a take masa shi ba.

A cikin daftarin kudurin nan na kare hakkin dan Adam na kasashen Turai, an hana yanke ko kuma zartad da hukuncin kisa a kan duk wani mahaluki, ko mene ne kuma laifin da ake zarginsa da shi. Kawo yanzu dai, kasashe 44 na nahiyar Turan ne suka sanya hannu kan wannan yarjejeniyar. Duk wata kasar da ke neman shiga cikin Kungiyar Hadin Kan Turai dai, dole ne ta soke hukuncin kisa daga tsarin dokokinta. Wannan sharadi ne da ya kamata a cika kafin ma a shiga shawarwarin amincewa da karbar kasar a cikin kungiyar.

A halin yanzu dai, nahiyar Turan ce kan gaba a duniya, wajen yin watsi da hukuncin kisa. Hakan kuwa na da asali ne, ta yin la’akari da irin goguwar da al’umman nahiyar suka yi da bala’o’in yakin duniya na farko da na biyu, da kuma irin gwagwarmayar da suka yi na kafa harsashen tafarkin dimukradiyya. A halin yanzu dai, duk shugabannin siyasa na nahiyar, tare da Majalisar Turai da kuma al’umman nahiyar gaba daya sun yarje kan wannan batun, na kau da hukuncin kisa daga tsarin dokokin kasashensu.

To amma, abin tambaya a nan shi ne, shi ke nan sai kasashen Turan su yi ta zaman oho ba ruwanmu, da irin cin zarafin bil’Adama da ake yi a kasashe da dama na ketare ? A ganin masharhanta da dama dai, bai kamata a kasance cikin wannan halin ba. Saboda a kasashe da dama na duniya, da inda ake mulkin dimukradiyya da inda ake kama karya, ana amfani da hukuncin kisan ne don cim ma wani buri na siyasa. A lal misali, har ma da kasashen da Kungiyar Hadin Kan Turai ke da kyakyawara ma’ammala da su a huskokin siyasa da na cinikayya.

A Amirka alal misali, batun hukuncin kisa na zamowa muhimmin jigo a lokacin yakin neman zabe. Ban da dai Japan, Amirka ce kasa mai bin tafarkin dimukradiyya, wadda kuma ta amince da zartad da hukuncin kisa. A ganin masana fannin nazarin dalilan aikata laifuffuka, wannan wani mataki ne na yi wa masu aikata laifuffukan gargadi da su kubuta daga aikata miyagun ayyukansu. Saboda duk wanda ya san hukuncin da za a yanke masa idan an same shi da wani laifi, kamar kisan kai, to mai yiwuwa ya kauce daga wannan danyen aikin.

Amma masu adawa da hukuncin kisan na nuna cewa, kafa dokar ma ba ta janyo ragowar masu aikata laifuffukan. Kuma, a wuraren da aka soke hukuncin kisan ma gaba daya, babu alkaluman da ke nuna cewa ana samun karin yawan masu aikata laifuffukan. A ganinsu dai, zartad da hukuncin kisa kan wanda aka same shi da laifin kisan kai, ba ya magance matsalar, ko kuma maido wa iyalan da suka yi asarar, dan uwansu. Bugu da kari kuma, akwai kura kurai da dama da ake yi a lokacin shari’ar, wadanda sai can da dadewa bayan an zartad da hukuncin ne ake gano cewa an yi kuskure.

A kasashen da ake mulkin kama karya ne kuma dai aka fi yiin mafani da hukuncin kisan tamkar wata madogara ta cim ma burin siyasa. Ana iya ganin haka dai a wasu kasashen nahiyar Afirka da na yankunan Larabawa da na Asiya da kuma Sin. A galibi, a kan yanke wa dubannin jama’a a wadannan yankunan hukuncin kisa, kawai saboda sun bayyana ra’ayoyinsu na kin amincewa da manufar da masu mulki ke bi, bam a tare da basu damar kare kansu a kotu ba.

Kamata ya yi dai, a wannan rana ta yaki da hukuncin kisa ta Majalisar Dinkin Duniya, kasashen da ke kan gaba a wannan fafutukar, su kara ba da kaimi wajen angaza wa masu cin zarafin al’ummominsu da yanke musu hukuncin kisa ba tare da wata cikakkiyar hujja ba, da su kawo karshen wannan mummunan matakin. Babu shakka, ba a ko’ina ne za a iya cim ma nasarar janyo hankullan gwamnatocin kasashe su soke dokokin yanke hukuncin kisa ba. Amma, misalin Turai na nuna cewa, idan aka dage aka kuma nuna dauriya, to a hankali za a cim ma nasara.