1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar 'yan gudun hijira a tsibirin Malta

Zainab MohammedNovember 19, 2007

Shugaban Jamus Koehler ya bukaci tallafawa Afrika

https://p.dw.com/p/CJIK
Shugaban Jamus Koehler.Hoto: AP

Alokacin daya kai ziyara kasashen Mauritania da Algeria,shugaba Horst Köhler ya tattauna matsalar kauracewa nahiyar Afrika da ‘ya’yanta keyi,domin neman ingantacciyyar rayuwa a Turai ta kowace hanya,da magatan waɗannan kasashe.

A kowace sheakara dai kididdiga ya nunar dacewar akalla ‘yan afrika 2,000 ke kokarin ganin cewar sun shiga nahiyar turai kota wace hanya domin inganta rayuwarsu.Wanda hakan bazai kasa nasaba da dalilin dayasa alokacin ziyarar sa shugaba Köhler na nan tarayyar jamus ya tattauna da magabatan Mauritania da Algeria ba kan wannan matsala da hanyoyin da zaa maganta shi.

Bayan rangadin kasashen na Afrika dai shugaban na Jamus ya ziyarci tsibirin Malta wadda ke nahiyar turai,inda premien wannan birni Lawrence Gonzi ya godewa Jamus dangane da tallafawa tsibirin shawo kan wannan matsala ta kwararan baki ‘yan gudun hijira daga Afrika.Sai dai ya kushe kungiyara tarayyar turain dangane da rashin mayar da hankali kan matsalolin ‘yan gudun hijira.

Wannan tsibiri na Malta dake yankin Mediterian dai ,na mai zama wuri na farko da jiragen ruwa ɗauke da ɗaruruwan ‘yan Afrika dake neman shiga turai musamman lokacin rani,ke sauka.Da yawan alumma dubu 400 kachal dai,yanzu haka Malta da mai zama cibiyar ‘yan gudun hijira kimanin dubu 3,700,waɗanda ɗaruruwansu sun ,sunyi shekaru a sansanonin gudun hijiran,suna jiran dama na shiga nahiyar turai.

Wa mafi yawa daga cikin waɗannan yan gudun hijira dai basu da dalilin cigaba da zama a kasashensu,saboda rashin makama,kamar yadda Jonas mai shekaru 28 daga kasar Eritrea ya fadi.

“Akwai matsin lamba akan matasa kamar mu,domin dole ne kaje aikin sojiinda nan ne zaka kare rayuwarka,yana da matukar wahala saboda baa biyanka kuma baka da makoma,baka da ‘yancin magana akan gwamnati ,idan ka fadi wani magana na adawa da gwamnati zaa jefa ka a cikin kurkuku,kuma yadda ake yance hukunci a Eritrea babu adalci,kuma bamu yarda da hakan ba,shiya sa muka bar iyalan mu”.

Janas dai yayi karatu har ya zuwa makarantar gaba da sakandare.inda yayi aiki da waha hukumar mai,wanda da kuɗaɗen basa isansa sa ya ciyar da iyalainsa.Tun kafin shekaru 3 da suka gaba nedai wannan matashi ,ya ɗauki wannan mummunar hanya zuwa nahiyar Turai.

A yanzu haka dai yana tare da sauran ‘yan afrika dake tsibirin na Malta,waɗanda ke sansanin ‘yan gudun hijira a wani katafaren majami’ar roman katholika.Sai dai Wa Jonas zaman sa a Malta na gajeren lokaci ne.

“Manufa ta itace,saboda a kasata bamu da wata makoma,nazo turai domin inyi karatu domin inganta rayuta,domin in tallafawa marasa galihu na kasata”

A tsibirin na malta dake zama mafi karamar ƙasa a turai dai,akan samu baƙin haure kusan 800 a kowane wata waɗanda ke kokarin tafiya nahiyar turai don inganta rayuwarsu.

To sai dai wa shugaba Hörst Koehler waɗannan ‘yan gudun hijira suna da damar inganta rayuwarsu a kasashensu na haihuwa.

“Idan da za’a samu damar samarda ayyukan yi,yanayi na rayuwa a kasashensu na haihuwa zai fiye musu,wanda hakan kuma zai basu damar komawa gida.Idan kuwa babu yanayi na rayuwa mai kyau dole su hakura da wannan hali da suke ciki,koda yaya lalacewar sa.Adangane da hakane yake da muhimmanci a haɗa kai domin samar da taimakon raya kasashen na Afrika”