1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar yan gudun hijira na Iraqi

Hauwa Abubakar AjejeNovember 29, 2006

Yayinda ake ci gaba da zubda jini a Iraqi,dubban yan gudun hijirar kasar suna shiga cikin matsaloli a kasashe makwabta

https://p.dw.com/p/BtxH
Yan gudun hijira
Yan gudun hijiraHoto: AP

Ya zuwa yanzu dai miliyoyin yan Iraqi suka gujewa tashe tashen hankula a kasar,kasa kuma da suka fi zuwa itace kasar Jordan,wadda take karbar bakuncin ganawa tsakanin shugaban Amurka Bush da Nur al Malki firaministan Iraqin.

Sai dai wani rahoton kungiyar kare hakkin bil adama ta HRW yace dubban yan gudun hijira ta Iraqi dake Jordan tun 2003 da Amurka ta mamaye kasar suna fuskantar matsaloli wajen sake sabunta takardunsu na visa,wanda hakan yake janyo masu rasa matsayinsu na bakin halal a kasar.

Saboda haka rahoton ya nemi shugaba Bush daya matsawa Jordan ta taimaka saukaka matsalolin da yan gudun hijirar ta Iraqi suke fuskanta a Jordan.

Kakakin kungiyar ta Human Rights Watch a YGTT da arewacin Afrika Fadl al-Qadi ya baiyana DW cewa matsalar da yan gudun hijirar suke fuskanta abu ne daya kamata a maida hankali akai.

“ana cikin hali na kaka nikayi,muna da dubban yan Iraqi anan wadanda basu da aikin yi,babu hanyar karo ilmi,wadanda ake tilastawa komawa gidaa kullum wannan matsala ce babba.”

Kakakin gwamnatin Jordan Nasser Jawdeh yayi suka ga wannan rahoto yana mai cewa babu kashin gaskiya a cikinsa.

Ya kuma yi zargin cewa rahoton cewa dukkan yan Iraqi dake Jordan a matsayin yan gudun hijira suke wadanda kuma suke bukatar takardun visa kafin shiga kasar ta Jordan.

Gwamnatin Jordan tace akwai yan gudun hijira na Iraqi kusan rabin miliyan cikin kasar,sai dai rahotanni sun kiyasta yawansu ya kai 800,000.

Rahoton kuma na HRW yace Jordan da farko ta karbi yan Iraqin hannu biyu biyu amma daga bisani bayan harin bam din da aka kai wani otal a birnin Amman a watan nuwamba na 2005 sai jamian tsaro suka fara kamewa tare da maida wasu yan Iraqi wadanda basu da takardun zama zuwa kasarsu.

Kakakin kungiyar ya kara da cewa Jordan bata da niyyar kawo karshen wannan matsala.

“babu gamsasshen bayani kan yadda kasar Jordan zata dauki matakin magance wannan matsala,Jordan tana bukatar taimako sai dai bata nemi irin wannan taimako ba”

Duk kuwa da sukar Jordan darektan kungiyar a YGTT da arewacin Afrika Sarah Leah Whitson tace makwabtan Iraqi kamar Syria da Jordan su suka fi sassautawa yan gudun hijira ta Iraqi yankin.

Sai dai HRW ta zargi kasashen Amurka da Burtaniya da nuna halin ko in kula game da halin da suka sanya jamaar yankin sakamakon mamayar Iraqin da sukayi.

Darektar ta baiyana fatar cewa rahoton zai fargar da alummomin duniya su dauki nauyin kula da yan gudun hijirar Iraqi.

Tace su kuma kasashen Amurka da Burtaniya suna ganin cewa,amincewarsu da gagarinda miliyoyin yan gudun hijira na Iraqi ke ciki,kamar gazawa ce a garesu a kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Iraqi.