1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

matsalar yiwa mata fyade a kasashen dake fama da rikicin yan tawaye

Zainab A MohammadJune 22, 2005

Lardin Darfur a yammacin Sudan na daga cikin yankuna dake fama da wannan matsala ta azabtar da mata ta hanyar fyade

https://p.dw.com/p/BvbB
Hoto: AP

Kungiyar agaji na marasa lafiya a lardin Darfur dake Sudan,ta sanar da samun marasa lafiya mata kimanin 500,wadanda akayiwa Fyade ,acikin watanni hudu da suka gabata,kuma wannan kalilan ne daga cikin yawan mata da suka fada cikin wannan hali a wannan yanki.

Mataimakin sakatare general na MDD Jan Egeland ya fadawa wakilan komitin sulhun majalisar cewa,Mata da yara na cigaba da fuskantar matsaloli na fyade daga azzaluman maza a lardin Darfur,tare da kira ga hukumomin kasar Sundan dasu gaggauta daukan matakan ceton wadannan matan ta hanyar samar da tsaro da kariya wa fararen hula dake wannan yanki dake fama da rikicin mayaka.

A jawabinsa wa komitin dangane da bukatar kasashen duniya su taimaka wajen kare alummomin fararen hula a yankuna da ake fama da rikicin mayaka,mr Egeland ya bayyana Sudan da Jasnhuriyar democradiyyar Congo da kasancewa ,wadanda suka fi muni cikin kasashen rikici da akafi gasawa mata aya a hannu ta hanyar yi musu fyade,da azabtarwa.

Rikicin Darfur dai ya samo tushe ne shekaru biyu da suka gabatas,lokacin day an adawa suka dauki makamai domin yakan nuna wariya da gwamnati ke musu.Ana dai zargin gwamnatin Khartum da mayar da martini da mayakan sakai,wadanda suka kone kauyukan yan adawan da kashe kasha da kuma yiwa mata fararen hula fyade.

Akalla kididdiga na nuni dacewa mutane dubu 180 suka rasa rayukansu a wannan rikici daga yunwa da cututtuka ,ayayinda wasu miliyan biyu suka tsere da rayukansu.

Mr Egeland yace kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontieres ta ruwaito ceto mata 500 da suka fada hannu miyagun mazajen ta hanyar fyade cikin tsukin watanni hudu da suka gabata kadai.

Jamiin na majalisar dunkin duniya yace wannan wadanda suka gabatar da kansu ne kadai domin neman magani,Allah kadai yasan yawan wadanda suka fada cikin hali makamancin wannan,kana abun takaici injishi,shine yadda gwamantin Sudan ta kasa yin wani abun kuzo ku gani dangane wadannan matsaloli balle daukan matakan magantasu.

Ya kara dacewa bawai kariya kadai ne gwamnatin Sudan ta kasa samarwa ba,wasu mata marasa aure da suka samu juna biyu daga ire iren wadannan fyade,kan fada wasu matsaloli na azabtarwa,daga hannun jamian tsaro na gwamnati musamman yansanda.

A dangane da hakane mataimakin sakataren mdd ya bukaci kasashen duniya dasu taimaka wajen shawo kan wannan lamari.

Ayayinda a nasu bangare wakilan komitin sulhu na Mdd suka bukaci kotun sauraron manyan laifuka na kasa da kasa data binciki wadannan miyagun ayyuka da ake aikatawa a lardin darfur.Idan zaa iya tunawa a farkon wanna wata nedai gwamnatin Sudan ta sanar da kafa kotu wadda zata hukunta wadanda keda hannu cikin laifuffuka miyagu a lardin na Darfur dake yammacin kasar.