1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar yunwa a nahiyar Afirka

February 20, 2006

A galibi dai, nahiyar Afirka ta dade tana fama da bala'in yunwa da fatara. Amma wai shin wannan matsalar babu wata hanyar shawo kanta ne ? Idan aka dubi lamarin da idon basira za a ga cewa, a wasu lokutan sakacin gwamnatocin kasashen nahiyar ne ke janyo irin wanna bala'in.

https://p.dw.com/p/BvTn
Mata a kasar Habsaha, suna jiran taimakon abinci.
Mata a kasar Habsaha, suna jiran taimakon abinci.Hoto: AP

Samun isashen abinci dai, hakki ne na ko wane dan Adam. kasashe dari da 51, mambobin Majalisar Dinkin Duniya ne suka sanya hannu kan wannan manufar, wadda ke kunshe cikin ka’idojin tattalin arziki, da na jin dadin zaman jama’a da al’adu, da Majalisar ta tsara kuma ta gabatar. Amma a galibi, gwamnatocin kasashe da dama na take wannan hakkin da bil’Adama ke da shi na samun isashen abincin. A halin yanzu, mutane kusan miliyan 11 ne ke fama da yunwa a kasashen gabashin Afirka, wadanda suka kama daga Eritrea har zuwa Tanzaniya. Wani mummunan farin da ba a taba yi ba tun shekaru 10 da suka wuce a yankin, ya kara tabarbare al’amura a kasashen na gabashin Afirka. Amma, kafin irin wadannan annobobin su auku, ana ganin alamunsu, a kuma yi gangami. Sai dai, a galibi mahukuntan kasashen ne ba sa daukan matakai a lokaci sai aski ya kai gaban goshi.

A nahiyar Afirka ne dai, irin wannan matsalar ta fi tsamari. kasashe kamarsu Sin da Indiya, sun tsara wasu shirye-shirye na tinkarar annoba kamar fari da yunwa tun da wuri. Duk da hakan dai, a wadannan kasashen ma, musamman ma dai a Indiya, da Brazil da kuma dai kasashen Afirka kamarsu Uganda, kai har da ma Afirka Ta Kudu, ba a bai jama’a cikakkun hakkinsu na samun abinci. Gaba daya dai, za a iya cewa, ko’ina aka waiwaya a nahiyar za a ga yaduwar yunwa da fatara. A halin yanzu dai, kasashe 32 daga 52 na nahiyar ne ke dogara kan taimakon abinci daga ketare.

A wasu ksashen dai, a kan sami sassaucin lamarin. Amma a yankunan da ake ta yake-yake, wannan ma kawai matsala ce. To idan kuma aka sami karancin ruwan sama, har ya kai ga fari, sai al’amura su kara tabarbarewa. Haka ne dai lamarin yake a kasashe kamarsu Somaliya, wadda har ila yau ba ta da tabbatacciyar gwamnati, da kuma Habasha. A Habsahan ma, matsalar yunwar na da asali ne daga gwamnatin kasar. Saboda, tana kashe dimbin yawan kudaden da za a iya yin amfani da su a harkokin bunkasa noma, wajen sayen makamai don ci gaba da yakin da take yi da Eritrea.

A kasar Kenya kuma, sakacin gwamnatin ne ke janyo yunwa da rashin abinci a wasu yankunan kasar. A yammacin kasar dai, ana noman isashen abinci musamman ma masara. Amma gwamnati ba ta da wani tsari na jigilar kayan abincin da aka noma daga wannan jihar zuwa sauran yankuna na kasar da ke huskantar fari da karancin ruwan sama.

Akwai dai dalilai da dama da ke janyo bala’in yunwa, kama daga yaduwar hamada, zuwa canje-canjen yanayi da kuma salon nan na hadayyar tattalin arzikin duniya, wanda ke karya darajar kayayyakin noma a kasashe masu tasowa. Fiye da mutane miliyan dari 8 a kasashe masu tasowan ne dai wannan matsalar ke shafa.