1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar yunwa a Somaliya ta dauki hankalin jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar
March 10, 2017

Batun yunwa a Somaliya da na 'yan adawa a Zimababwe, zuwa adadin mutanen da suka mutu a rikicin Boko Haram a Najeriya ne suka mamaye sharhunan jaridun na Jamus a wannan mako.

https://p.dw.com/p/2YxRy
Somalia Hunger und Cholera fordern  mindestens 110 Todesopfer
Jerin mata masu jiran karbar abinci a SomaliyaHoto: picture alliance/AP Photo/F. Abdi Warsameh

 A sharhin da ta rubuta mai taken "An yi kunnen watsi da gargadin da aka yi", jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce miliyoyin mutane ne ke fuskantar barazanar yunwa a yankin gabashin Afirka. Majalisar Dinkin Duniya ta yi shelar barazanar matsananciyar yunwa da kasar Somaliya da ma wasu sassa na kasashen Afirka ke fuskanta.

Antonio Guterres ya yi kashedi daga Somaliya

Somalia Mogadischu - U.N. Generalsekretär Antonio Guterres bei Pressekonferenz
Sakataran Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da shugaban Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed.Hoto: Reuters/F. Omar

A wata ziyarar da ya kai Mogadishu babban birnin Somaliya, Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi nuni da cewar duniya na kallon wannan bala'i na yunwa na ci gaba da ta'azzara a Somaliya. Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewar sama da mutane miliyan shida a Somaliya kadai, adadin da ke zama rabin al'ummar kasar na bukatar agajin gaggawa.

Guterres ya ce hankalin duniya ya koma kan rikicin Siriya, wanda a fakaice ya boye halin da wannan kasa da ke yankin kahon Afirka ke ciki na matsananciyar wahala. Daura da matsalar yunwa da karancin abinci, kasar ta Somaliya na fama da barkewar cututtuka kamar na amai da gudawa da kuma cutar kyanda kamar yadda hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta nunar.

Kotu ta sallamo 'yan adawa a Zimbabwe

Simbabwe Harare Proteste gegen Präsident Mugabe
Masu adawa da Shugaba Mugabe a ZimbabweHoto: picture-alliance/AA

Sai kuma kasar Zimababwe inda kotun kasar ta sallami wasu masu adawa da gwamnati akalla 65 da aka tsare. A sharhin da ta rubuta kan wannan lamari, jaridar Die Tageszeitung, ta ce a ranar Talatar wannan mako mai karewa ne alkalin wata kotu a birnin Harare ya bada umarnin sakin masu zanga-zangar adawa da cin hanci da karbar rashawa da wadaka da dukiyar kasa. Daga cikin wadanda kotun ta wanke har da wasu yara matasa 'yan tsakanin shekaru 16 zuwa 19 daga unguwar marasa galihu ta Epworth da ke Harare.

Za mu karkare sharhin na wannan makon da Tarayyar Najeriya, inda Jaridar Süddeutsche Zeitung ta buga wani sharhi mai taken " Me ya sa yake da wuya a samu yawan wadanda rikicin ta'addanci ya ritsa da rayukansu?" A cewar jaridar, furucin gwamna Kashim Shettima na jihar Borno na cewar mutane dubu 20 ne suka rasa rayukansu tun daga barkewar rikicin Boko Haram a shekara ta 2009 kawo yanzu, ba abun amincewa ba ne.