1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar yunwa ta ritsa da dubban mutane a Najeriya

February 9, 2017

Wani sabon rahoton shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa dubban mutane za su yi fama da karancin abinci sanadiyar rikicin Boko Haram cikin yankin arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/2XGdp
Nigeria Kind Unterernährung Ärzte ohne Grenzen
Hoto: picture alliance/AP Photo/Sunday Alamba

Wannan rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya yi hasashen cewar matsalar karancin abinci da ake fama da shi yanzu haka a sassan nahiyar Afirka musamman yankin arewacin Najeriya zai kara ta'azzara lokacin da ake kokarin samar da abinci wato a watannin Yuni da Agusta.

Nigeria Stadt Borno State
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Rahoton wanda na hadin guiwa ne tsakanin hukumar kula da ayyukan gona da shirin samar da abinci na majalisar dinkin ya nuna cewa jihar Borno ce zata fi fama da wannan matsala ta karancin abinci inda za a samu kashi 65% da wannan matsala ta shafa.
Rahoton dai ya nuna cewa rikicin Boko Haram ne musabbabin wannan matsala ta yunwa da karancin wanda ke zuwa a dai dai lokacin da daukacin sassan Najeriya ke kuka da matsalar yunwa da dankaren tsadar abinci abinda ya haifar da zanga-zanga a wasu sassan kasar.


Wannan rahoto dai ya nuna gamsuwa da cewar Gwamnatoci a jihohin shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya sun dauki matakai na ganin an samu sauki wannan matsalar amma akwai bukatar rubanya matakan. Alh Muhammadu Dili shi ne kwamishinan aikin gona na Jihar Borno ya bayyana cewa suna kokarin habaka noma musamman na rani don cike gurbin abin da aka rasa a damuna.

Symbolbild Nigeria Bama Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola


Najeriya dai tana cikin kasashen da ke fama da karancin abinci duk da albarkatun kasa da isassun filayen noma inda ake shigo da shinkafa da alkama kuma 'yan kasar na saye da tsada abin da ake alakantawa da karuwar yunwa da yanzu haka al'ummar kasar ke fama da shi.