1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar zirga-zirga a iyakar Tunisiya da Libiya

Salissou BoukariMay 3, 2016

Hukumomin kasar Libiya sun dakatar da shigar duk wasu kayayyaki daga mashigar Ras Jedir da ke kan iyakar kasar da Tunisiya tsawon kwanaki da dama.

https://p.dw.com/p/1Ih98
Grenzstellenübergang Rass Jdir in Tunesien an der Grenze zu Libyen
Mashigar Ras Jedir a tsakanin Tunisiya da LibiyaHoto: Reuters/Zoubeir Souissi

Rahotanni daga yankin Zarzis na kasar Tunisiya na cewa, harkokin zirga-zirgar kasuwanci sun tabarbare a kan iyakar kasar da Libiya tun yau da kwanaki biyar bisa umarnin hukumomin kasar ta Libiya a cewar hukumomin kasar Tunisiya. Ita dai mashigar kan iyaka ta Ras Jedir ta kasance wata hanya muhimmiya da ke hada yankin yammacin kasar Libiya da kuma Kudu maso Gabashin kasar Tunisiya, yankunan da ke rayuwa da harkokin hada-hadar kasuwancin da ake yi tsakanin kasashen biyu.

Tun dai daga ranar Jumma'a ce harkokin zirga-zirgar suka shiga cikin wani mawuyacin hali, bayan da hukumomin kasar Libiya suka hana shigar da duk wasu kayayyaki ya zuwa kasarsu. Kawo yanzu dai ana ci gaba da tattaunawa tsakanin kungiyoyin fararan hula da kuma wakillan hukumomin kasashen biyu a cewar Gwamnan jihar Medenine Tahar Matmati.