1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MATSALOLIN DA KOGIN NIGER KE FUSKANTA

JAMILU SANIMarch 15, 2004
https://p.dw.com/p/BvlK
A halin yanzu dai an baiyana cewa kasahe na duniya da Allah ya horewa albarkatun ruwa da suka sha banban da wadanda suke da kanan tabkuna na fama da barazana iri dabam dabam,a sabili da rabin irin wadanan kasahe dake da albarkatun ruwa suka fuskanci matsaloli na gurbatar muhali a kusan fiye da shekaru 100 da suka gabata.
To sai dai kuma duk da wadanan matsaloli da kasahen dake da albarkatun ruwa ke fuskanta a halin yanzu,wasu daga cikin irin wadanan kasahe da suka saura dake da albarkatun na ruwa,nada muhimancin gaske ga rayuwar bil adama.
Kogin Niger ga misali dake zaman na biyu mafi girma a nahiyar Africa,na fama da matsaloli a sabili da yawan kasahe dake amfani da wanan tabki na Niger,baya kuma ga rashin amfani da irin wadanan albarkatu na ruwa da ake da su yadda ya kamata,bayan wasu matsalolin kuma da suka shafi malalar yashin Hamada.
A halin da ake ciki dai matsaloli na malalar yashin Hamada ya sanya gabar kogin na Niger ta zama wani dandali na tarin yashi dake zaman wata babar barazana ga harkokin kamun kifi. Duk kuwa da wadanan matsaloli da ake fuskanta a kogin na Niger,kasahen da wanan kogi ya ratsa ta cikin su,ga misali a iya cewa gabar wanan kogi data ratsa ta kasar Swizland zuwa kasar mali,a iya cewa gabar wanan kogi dake cikin wadanan kasahe biyu basa fama da wata matsala kamar yadda lamarin yake a a jamhuriyar Niger dake fama da matsaloli na malalar yashin Hamada. Tbkin dai na Niger na zaman yankin ruwan da ya ratsa kasahe da dama na Africa ta yamma,yayin kuma da wanan kogi ke zaman na uku mafi tsawo da ake da shi a nahiyar Africa baki daya wanda kuma bi ta kasahe irin su Guinea da da kuma Nigeria.
A kasar mali kogin dai na Niger da ya ratsa ta wasu yankuna kasahen Sahel zuwa kasar ta Mali,shekaru masu yawa da suka shude ya zamanto,mai matukar amfani ga alumar wanan kasa dake sana'ar kamun kifi.
A tabakin wani masunci na kasar ta mali,ya baiyana cewa wanan tabki na Niger shine rayuwarsa,,kuma ya dogara da shine wajen samun abinda zai ciyar da iyalansa.
Ya dai baiyana cewa yana gudanar da sana'ar kamun kifi ne ta gabar wanan kogi na Niger da ya ratsa ta cikin kasar su.To sai dai kuma a wasu wuraren ana samun yashi mai yawa,don haka akwai fargabar cewa za'a iya fusakantar masala ta kamun kifi matukar dai yashi cigaba da karuwa a gabar wanan kogi na Niger.
Babar Matsalar da ake fuskanta dai ita ce ta yawan yashi dake barazana ga kogin na Niger,ta yadda hakan ka iya zama babar barazana ga kasahen da wanan kogi ya ratsa ta cikin su.Wanan matsalai ta karwar yashi a kogin na Niger zata iya sanyawa a yi asarar nau'oi na halitu da Allah madaukin sarki ya ajiye a karkashin kasa,baya kuma ga tsirai na ciyayi da ake amfani da su wajen hada magunguna.
A sabili hakan ne Denis Landenbergue manajan kungiyar kare albarkatun ruwa ta kasa da kasa Wetlands Conservation ke ganin gwamnatocin kasahen da kogin na Niger ya ratsa ta cikin su na bukatar agajin kudade domin yaki da yashin na kogi,wanda kuma aka baiyana da cewa na haifar da matsaloli na dumamar yanayi,fari da kuma yawan ruwan da ake bukata don amfanin yau da kulum.