1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalolin rayuwa na dada durkushewa a Zimbabwe

Zainab A MohammadDecember 28, 2005
https://p.dw.com/p/Bu2x
Shugaba Robbert Mugabe na Zimbabwe
Shugaba Robbert Mugabe na ZimbabweHoto: dpa

Yan kasar Zimbabwe na shirin shiga sabuwar shekara cikin matsaloli na karancin abinci da karuwar durkushewar tattalin arziki,ayayinda a hannu guda kuma babu alamun warwarewar matsalolin siyasa.

Ayayinda shugaba Robbert Mugabe ke ikirarin ingantuwan tattalin arzikin kasar da kashi 3 da digo 5 cikin 100 a shekaras ta 2006,manazarta kann harkoki na tattalin arziki da yan Zimbabwe na ganin cewa wani matsanancin hali na rayuwa ne kasar zata sake fadawa.

Manazarci kann harkokin tattali a kasar John Robertson yace matsaloli da Zimbabwe ta kasance ciki a ashekaru 7 da suka gabata zasu cigaba da addabanta har cikin sabuwar shekarar da ake shirin shiga.

Shi kuwa shugaban kungiyar kwadago na kasa Lovemore Matonbo,cewa yayi babu komai da alummar kasar zasu kasance ciki a wannan sabuwar shekara face kunci na rayuwa,domin har yanzu gwamnati bata da masaniya kann yadda zata shawo kann matsalolin tattalin arzikin dake addaban kasar.

A kusan shekaru 10 da suka gabata dai,tattalin arzikin wannan kasa ya durkushe,sakamakon faduwar darajan kudi,da rashin aikinyi tsakanin alumma dayanzu ya haura kashi 70 daga cikin 100,baya matsaloli na karancin abinci da man petur.

A ta bangaren siyasa kuwa,darewa da babbar jammiyar adawa ta MDC tayi ya karya karfin jammiiyar dake kasance babbar barazana ga shekaru 25 na mulkin Mugabe a baya.

Manazarci kann harkokin siyasa a zimbabwe Bill Saidi yace matsalolin siyasa dake addabar jammiyar adawa ta MDC,ya dakatar da ita daga kasancewa babbar makami na kalubalkantar gwamnati.

A watan febrairu nedai akesaran cewa jammiyar adawar zata gudanar da taron ta shekar shekara,ibnda ake kyautata zaton gano bakin zaren warware rikicin daya tarwatsa jammiyar.

A watanni masu gabatowa dai mdd zata bada agajin abinci wa alummar Zimbabwe kimanin million 3,a wannan kasa data taba kasance mai ciyar da kudancin Afrika baki daya.

Gwamnati dai na ciga da danganta karancin abincin da matsalar fari,amma manazarta nacewa kwace gonakin fararen fatu yan kasuwa da akayi a 2000 tare da sake rarrabawa babaken kasar ne yxa haifar da wannan matsala a sashin noman kasar.

A dangane da Hakane Mr Robbertson ke ganin cewa a bana kasar zata fuskancin mummunan girbi ,saboda manoma basu samu kyayyakin aiki akan lokaci,batu dake nuni dacewa ana bukatar karin kudade na shigar da abincin da kasar zata iya nomawa.

Yanzu yan kasar na ganin cewa babu wata madogara ,domin kasashen yammaci dake kasuwanci da Zimbabwe sunyi watsi da ita ,tun daga zaben shugaban kasa a shekara ta 2002,wanda masu gani da ido sukace an tabka magudi da arangizon kuriu.

Akan hakane Mr Saidi yana mai raayin cewa dole ne Zimbabwe ta sake hadewa da kasashen ketare ta hanyar warware takaddama dake tsakaninsu,idan ba haka ba kuwa,zasu cigaba da kasancewa cikin matsalolinsu.