1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalolin 'Yan Afurka A nahiyar Turai

September 7, 2004

A cikin wata hikayar da ta rubuta Fatou Diome daga kasar Senegal tayi bayani filla-filla a game da matsalolin da 'yan Afurka ke fama da shi a nahiyar Turai da kuma barazanar da suke fuskanta akan hanyarsu ta shigowa nahiyar

https://p.dw.com/p/Bvgh

Wannan matsalar ta fafutukar yin kaura zuwa nahiyar Turai ita ce ginshikin wata hikayar da wata ‚yar kasar Senegal mai suna Fatou Diome ta rubuta baya-bayan nan. Wannan hikaya na batu ne a game da wani da ake kira Madicke, wanda ba abin da ya kudurta a zuciyarsa illa ya tattara nasa ya nasa ya kaurace daga kauyensu zuwa kasar da ke da wadatar da hada kowa da kowa hatta jariran da suka fara rarrafe. Amma fa a hakikanin gaskiya lamarin ba haka yake ba kuma murna ta kan koma ciki bayan mutum ya shigo wannan nahiya a cewar Fatou Diome marubuciyar hikayar. A lokacin da take bayani jami’ar karawa tayi da cewar a hakikanin gaskiya wasu daga cikin ‚yan Afurkan da kan yi kaka-gida a nahiyar turai su kan yi tsawon shekaru biyar ko kuma suna masu tsumulmular kudi domin samun kafar kai ziyara gida. Da zarar sun isa kauyukansu kuma sai su rika yi tamkar dai tuni suka kudance basa yarda su fito fili su tsage gaskiyar mawuyacin halin da suke ciki a nahiyar Turai, inda su kan yi shekara da shekaru suna zama hannu baka-hannu kwarya. Wajibi ne a wayar da kan jama’a a game da cewar ita Turai fa ba Aljannar duniya ba ce kamar yadda mutane ke zato. Duk mai sha’war rayuwa a cikin daraja da girmamawa to wajibi ne yayi zamansa a gida ko da kuwa yawan abin dake shiga hannunsa bai taka kara ya karya ba. Akwai abubuwa masu tarin yawa da mutum ke samu a cikin sauki a nahiyar Afurka, amma ba zai san darajarsu ba sai idan ya karaso nahiyar Turai. Bisa ga ra’ayin Fatou Diome akwai dalilai masu tarin yawa dake taka muhimmiyar rawa a game da fafutukar da ‚yan Afurka ke yi domin shigowa nahiyar Turai. Da farko dai finafinan da ake nunarwa ta gidajen telebijin da masu yawan bude ido dake yaduwa a gidajen otel ko kuma wasu bukkoki na kasaita da akan tanadar musu akan farashi mai rafusa. Yawa-yawanci an yi imanin cewar duk wani bature mawadaci ne. A kasashe da dama na Afurka da suka wanzu karkashin renon mulkin mallaka an dauka cewar bature dai mutum ne da ya cika goma kuma saboda haka baya kuskure. Al’adu da yarensa sune a’ala da ya kamata a yi koyi da su. Wadannan mutane ba su da wata masaniya a game da cewar, ita ma nahiyar turai daidai da Afurka, tana mawadata dake da dimbim arziki da masu matsakaicin karfi da talakawa ‚yan rabbana ka wadata mu da jahilai da nakasassu da makamantansu. Ita dai Fatou Diome ta sikankance cewar makaurata daga Afurka zasu ci gaba da tuttudowa zuwa nahiyar Turai har ya zuwa lokacin da Allah zai wayar da su. Wadannan makaurata zasu ci gaba da neman duk wata hanyar da ta sawwaka a garesu domin shigowa Turai ko da kuwa zasu sadaukar da rayukansu ne. Amma shawara daya da zata ba wa mahukunta shi ne duk wani dan Afurka da aka cafke domin komawa da shi gida to a ba shi wani dan abin da zai iya jari da shi, domin kuwa duk wanda zai iya ci da kansa ba zai nemi abinci daga wani ba.