1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin nukiliyar Koriya ta Arewa

May 27, 2009

Hukumomin Amirka sun bayyana aniyar hauwa tebrin shawara da na Pyong Yang a game da rikicin nukiliya.

https://p.dw.com/p/HyfM
Shugaba Kim Yong Il na Koriya ta ArewaHoto: picture-alliance/ dpa

Duk da matakin da Koriya ta Arewa ta ɗauka, na cigaba da gwajin makaman nulkiya, Amurika tace a shirye take ta hau tebrin shawara da hukumomin Pyong Yang, da zumar warware wannan taƙƙadama.

Bayan gwajin makamain nukiliyar da suka ƙaddamar, hukumomin Korea ta Arewa sun cigaba da ɗaga murya tare da yin wasti da kiran-kiranyen da Amurika da Majalisar Ɗinkin Duniya ke matsu domin su dakatar da wannan harbe harbe.

Saidai duk da haka, a cewar Ian Kelly, kakakin Sakatariyar harakokin wajen Amirka, fadar Washigton a shirye take ta hau tebrin shawara da Koriya ta Arewa, domin magance wannan matsala:Siyasar da gwamnatin mu ta ɗauka a game da wannan batu shine, kusantar hukumomin Koriya ta Arewa, domin su mutunta dokokin ƙasa da ƙasa wanda suka umurce su, su yi watsi da makamin nukiliya da kuma gwajin da suke yi.

Mai haƙuri ya kan dafa dutse, kuma ƙofofi a bude suke, muna fata Koriya ta Arewa,zata yi amfani da wannan dama domin cimma masalaha.

A yayin da ya gabatar da jawabi a game da wannan batu, shugaban ƙasar Amirka Barack Obama yace ba za shi ƙasa a gwiwa ba, kuma zai amfani da ma´amilarsa da abokan arziki, kamar su Rassha sda China ke da hulɗoɗin ƙut da ƙut da Koriya ta Arewa:za mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙasashe amminai, domin tankoso hukumomin Koriya ta Arewa su bi doka da oda, a ɗaya wajen, ina kira da babbar murya ga ƙasashen duniya su bada hadin kai domin cimma dutun dafawa.

Komitin Sulhu na Majaliasar Ɗinkin Duniya, ya bayyana aniyar ɗaukar wani saban mataki na ladabtar da Koriya ta Arewa, bayan gwajin makaman nukiliyar da ta yi, to saidai ƙasashen Rasha da China, kamar yadda suka saba, sun bayyana adawa.

Jikadan Koriya ta Arewa a Majalisar Ɗinkin Duniya, yace ƙasashen da kai gwabro da mari ,domin hukunta ƙasarsa ba su yi mata adalci ba,yaci gaba da cewa:Abinda ke da mahimmanci shine a daina ɓaɓatun da bai dace a game da wannan batu, mussamman a ɓangaren Amirka da Japan.Bamu da wana mummunar manufa, a cikin wannan shiri illa kawai mun kare kanmu.

A halin da ake ciki dai yanzu ,wannan rikici ya ɗauki saban sallo, bayan da shugaba Kim Jong Il na Koriya ta Arewa ya bayyana janyewar ƙasarsa daga yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekara ta 1953, tare da Koriya ta Kudu, sannan ya ambata yiwuwar kai hari ga ƙasar maƙwabciya.

Tun shekaru shidda da suka gabata, aka fara tattawar da ta ƙunshi ɓangarorin shidda wato Amirka, Rasha, Japan, China, da Koriya ta Arewa da kuma Koriya ta Kudu.

To saidai tun watan Afrilu da ya gabata, Koriya ta Arewa ta fice daga wannan shawarwari domin nuna fushi, a game da matakin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɗauka, na yin Allah ga gwajin makamin Nukliyar da Koriya ta Arewa tayi, ranar biyar ga watan Afrilu.

Mawallafi:Sina Ralph/ Yahouza Sadissou.

Edita: Mohamed Nasiru Awal