1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton shekara na hukumar kare haƙƙin bil Adama ta Duniya.

Tanko Bala, AbdullahiJanuary 31, 2008

Hukumar kare haƙƙin bil Adama ta Duniya "Human Rights Watch" ta yi kakkausar suka ga ɗaurewa shugabannin kama karya gindi da sunan dimokraɗiyya

https://p.dw.com/p/D0dy
Kenneth Roth, Shugaban Hukumar kare haƙƙin bil Adama ta Duniya ke bayani wajen gabatar da rahoton hukumar na shekarar 2008Hoto: AP

Hukumar ta Human Rights Watch ta ce barin irin shugabanin kama karya akan karagar mulki da sunan dimokradiyya ba tare da tabbatar da cewa suna aiwatar da matakan wanzar da dimokraɗiyyar ba, tamkar karan tsaye ne Amirka da ƙasashen Turan suke yiwa tafarkin na dimokraɗiyyar. Rahoton yace wajibi ne ƙasashe irin su Kenya da Pakistan su tabbatar da kare haƙƙin alúma ba kawai su riƙa furtawa da baki cewa su masu son cigaban dimokraɗiya ne ba.


Hukumar kare haƙƙin bil Adaman ta duniya ta ce a shekarar 2007 alal misali gwamnatoci da dama da suka haɗa da Baharin da Jordan da Nijeriya da Rasha da kuma Thailand sun nuna tamkar gudanar da zaɓe shine cewa suna dimokradiyya. Kenneth Roth babban daraktan hukumar kare haƙƙin bil Adaman ta duniya yace a yanzu kusan ya zama ruwan dare shugabanni su fake da sunan dimokraɗiyya a gefe guda kuma suna aikata akasin hakan.


A dangane da Nijeriya, rahoton na Human Rights Watch ya yi nuni da taɓargazar cin hanci da rashawa da cin zarafi da yan sanda ke yiwa jamaá fararen hula. Bugu da ƙari ya kuma tunato yadda aka yi amfani da jamián tsaro da yan banga a lokacin zaɓen 2007 da ma yadda aka tafka maguɗi a zaɓen wanda a baiwa shugaba Umaru Musa Yar Aduá na jamíyar PDP nasara da gagarumin rinjaye. Rahoton ya ƙara da cewa saboda tasirin da Nijeriya ke da shi da kuma matsayin ta, Amirka da Britaniya da ƙungiyar gamaiyar Afirka dana ƙasashe renon Ingila Commonwealth suka gaza taɓuka komai ko yin Allah wadai ga keta haddin bil Adama a ƙasar.


Game da halin da ake ciki a ƙasar Kenya kuwa, rahoton ya baiyana rikicin da ya biyo bayan zaɓen da aka gudanar a ƙasar da cewa yana neman wargaza ƙasar saɓanin tunani ko buƙatar alúmar waɗanda suka fito ƙwansu da ƙwarkwata suka kaɗa ƙuriá bisa tafarki na dimokraɗiyya. Yana mai cewa wajibi ne shugabannin biyu Odinga da Kibaki su sanya buƙatar alúmar ƙasa akan dukkan wata buƙata tasu ta daban domin samun ɗorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.


Marian Heuwagen jamiá a ofishin hukumar kare haƙƙin bil Adaman dake birnin Berlin a nan Jamus ta yi bayani tana mai cewa sun damu matuƙa dangane da yadda ƙasashe masu zaunanniyar dimokraɗiyya kamar Amirka da tarayyar Turai basa sa baki a inda ake take haƙoƙin jamaá da batutuwan Dimokraɗiya a ƙasashe da dama Ko kuma halin da ake ciki yanzu a ƙasar Kenya. Da ta juya ga ƙasar Chadi, Marian Heuwagen tace babban fata shine dakarun da ƙungiyar tarayyar Turai za ta tura zuwa Chadi, za su taimaka wajen rage rikice rikice da fyaɗe da wahalhalun da mutane ke fama da su musamman a ɓangaren yan gudun hijira da suka rasa matsugunan su .