1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin Jamus bayan taron birnin Rom kan Lebanon

YAHAYA AHMEDJuly 27, 2006

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier, ya yi wa kwamitin kula da al'amuran ƙetare na majaliar dokoki ta Bundestag, bayanai kan sakamakon da aak cim ma a taron ƙasa da ƙasa kan ƙasar Lebanon wanda aka gudanar a birnin Rom a ran larabar da ta wuce.

https://p.dw.com/p/Btyr
Ministan harkokin wajen Jamus, Frank Walter Steinmeier
Ministan harkokin wajen Jamus, Frank Walter SteinmeierHoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Mambobin kwamitin kula da al’amuran harkokin waje a majalisar dokoki ta Bundestag dai, sun fi mai da hankalinsu ne kan yadda tsarin dakaraun ƙasa da ƙasa da za a girke a kudancin Lebanon zai kasance. A taron ministocin harkokin wajen ƙasa da ƙasa da aka yi a birnin Rom jiya ne aka yarje kan tura dakarun zuwa Lebanon. A yau ne kuma, ministan harkokin wajen Jamus, Frank Walter Steinmeier, ya gabatar wa kwamitin majalisar cikakken rahoto kan yadda aka gudanar da taron na birnin Rom. Bayan taron kwamitin, wanda aka yi a bayan shinge, ministan harkokin wajen na Jamus ya yi fira da maneman labarai, inda ya bayyana musu abin da ya kira gundarin shawarwarin da aka yi a birnin Rom:-

„Gundarin shawarwarin dai shi ne ƙarfafa wa gwamnatin ƙasar Lebanon gwiwa, abin da ke nufi ke nan, ƙarfafa wa rundunar sojin ƙasar ma gwiwa, don ta iya samun damar tabbatad da tsaro a kudancin ƙasar da kuma kan iyakarta da arewacin Isra’ila. Don cim ma wannan burin ne za a bukaci wanzuwar dakarun ƙasa da ƙasa a yankin, waɗanda za su tallafa wa Lebanon da rundunar sojinta wajen iya gudanad da wannan aikin.“

Kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin Jamus dai, ya bayyana ra’ayin cewa, bai kamata a rataya wa rundunar dakarun ƙetaren nauyin kwance wa Hizbulahi ɗamara ba. Aikinsu zai kasance hana Hizbullahin ne sake komawa gurabansu kusa da iyakar Isra’ilan. Amma rundunar sojin ƙasar Lebanon ɗin ce ke da nauyin kwance wa Hizbulllahin ɗamara, ƙarƙashin ƙuduri mai lamba 1559 da Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartar. Har ila yau dai, ba a san yadda dakarun ƙetaren za su iya tallafa wa rundunar sojin Lebanon wajen gudanad da wannan aikin ba.

’Yan adawa a majalisar dokokin, sun yi kakkausar suka ga mahalarta taron Rom da kuma na St. Petersburg, saboda gazawarsu wajen yin kira ga tsagaita buɗe wuta ba da wani sharaɗi ba a yankin Gabas Ta Tsakiya. A ko wace ranar da ake fafatawa dai, kasadar yaɗuwar rikicin zuwa sauran yankunan Gabas Ta Tsakiyan sai ƙaruwa take yi, inji Kerstin Müller, kakakin jam’iyyar Greens a kan batutuwan harkokin ƙetare. Ta dai goyi bayan matsayin da ministan harkokin wajen Jamus ya ɗauka, na yin watsi da da wata sanarwar da ministan shari’a na Isra’ila ya bayar, wadda ke jaddada cewa, taron na Rom ya amince wa ƙasarsa da ta ci gaba da farmakin da take kaiwa a Lebanon.

Bayan taron birnin Rom ɗin dai, ministan harkokin wajen Jamus, Frank Walter Steinmeier ya ce duk mahalartan sun yarje kan girke dakaru a kan iyakar Lebanon da Isra’ila:-

„Duk waɗanda suka halarci taron jiya, wato ƙasashe 15, da Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, sun yarje kan cewar, girke dakarun kaɗai ne tabbataciyar hanya, ta kai ga kwantad da ƙurar rikici da kuma tsagaita buɗe wuta.“

Ministan ya kuma kyautata zaton cewa, a cikin mako mai zuwa, Majalisar Ɗinkin Duniya za ta zartad da ƙuduri na girke dakarun. To sai dai, Jamus ta ce a halin yanzu, ba za ta ce uffan ba game da ba da gudummowar dakarunta ga rundunar ƙasa da ƙasar, sai Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartad da ƙudurinta tukuna.