1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin Jamus Game Da Iraki

June 28, 2004

Jamus a shirye take ta ba da gudummawa wajen sake gina Iraki, amma ba zata tura sojojinta domin aikin kiyaye zaman lafiya a wannan kasa ba

https://p.dw.com/p/Bvid
P/M wucin gadi na kasar Iraki
P/M wucin gadi na kasar IrakiHoto: AP

Gwamnatin Jamus dai har yau tana kan bakanta na kin tura sojojinta zuwa kasar Iraki, ko da yake a shirye take ta ba da gudummawa iya mustada’a domin sake gina kasar da yaki yayi kaca-kaca da ita. Daga cikin gudummawar da Jamus zata iya bayarwa har da ba da horo ga jami’an tsaron kasar Iraki. To sai dai kuma horon zai iya samuwa ne a hadaddiyar daular larabawa a maimakon a kasar Iraki saboda tabarbarewar tsaro a kasar. An saurara daga bakin shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder yana mai nuna cewar, a baya ga ‚yan sanda, kasar a shirye take ta ba da horo ga sojojin Iraki idan har gwamnatin kasar ta bukaci hakan. Wannan shi ne taimakon da Jamus zata iya bayarwa amma ba zata tura sojojinta zuwa Iraki ba, ko da kuwa a karkashin tutar kungiyar tsaron arewacin tekun atlantika NATO ne, kamar yadda ministan harkokin waje Joschka Fischer ya kara da bayani, inda ya ci gaba da cewar:

2. O-Ton Fischer:

Ich bin der....

Na sikankance cewar dukkan sojojin kasashen yammaci da za’a tura zuwa Iraki zasu zama tamkar sojan mamaye ne a idanun al’umar kasar ta la’akari da yadda al’amura ke tafiya a cikin makonni da watannin baya-bayan nan. A saboda haka bai kamata ma a shiga wata mahawara ta tura sojan NATO zuwa kasar ta Iraki ba.

Tura dimbim sojojin ketare ba zai tsinana wa kasar Kome ba, muhimmin abin da ake bukata shi ne taimakon jinkai kuma Jamus a shirye take ta yafe wa Irakin wani bangare na basussukan da take binta. Kasashen Jamus da Faransa ba su dadara ba suna masu gabatar da kira ga kasar Amurka da ta ba wa MDD ikon sa ido akan wasu sahihan matakai da za a tanada domin sake mayarwa da kasar Iraki cikakken ikon cin gashin kanta. An shigar da wannan maganar a kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya gabatar baya-bayan nan akan kasar Irakin.

Amma fa wannan maganar ba ta ma’anar cewa Jamus na neman ganin Amurka ta shiga garaje wajen janye daukacin sojojinta daga kasar Iraki, musamman ma ta la’akari da halin na zaman dardar da kasar ke ciki. Wannan halin ne ya sanya gwamnati a fadar mulki ta Berlin ta ce ba zata tura sojojinta zuwa kasar ta Iraki ba take kuma gabatar da gargadi ga matafiya da su kaurace wa wannan kasa. Akwai alamomin dake nuna kara tabarbarewar al’amura bayan samun ikon cin gashin kan kasar, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Jamus ta nunar.