1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin majalisar Bundestag akan taimakon raya ƙasa.

June 19, 2010

Damuwar majalisar Bundestag ta rashin cimma manufar raya ƙasa.

https://p.dw.com/p/NxUn
Majalisa dokokin Jamus(Bundestag).Hoto: picture alliance/dpa

Majalisar dokokin Jamus ta nuna damuwa game da tafiyar hawainiya da muradun rage talauci a ƙasashe masu tasowa da Majalisar Ɗinkin duniya ta tsara ke yi. Ita dai Bundestag a zamanta na mahawara ta nunar da cewa burin inganta ilimi da kiwon lafiya a ƙasashe matalautan ba zai cika ba, sakamakon kasa cika alƙawuransu da ƙasashe da ke ba da agaji suka yi, ciki kuwa har da Jamus.

Jamus ta ba da taimakon raya ƙasa abin da ya kai Euro miliyan dubu shidda ne a shekara ta 2010, Ko da shike wannan adadi ne da ba'a taɓa samun irin sa ba, amma gwamnatin haɗin-gwiwa da ke ci a yanzu, ta kasa cika alƙawarin da gwamnatin da ta gaji mulki a hannunta tayi, na ware abin da ya kai rabin kashi ɗaya cikin ɗari na kuɗaɗen da ƙasar take samu a shekara a matsayin taimakon raya ƙasa. Gaba ɗaya a bana, ba'a sa ran wannan adadi zai wuce ɗigo huɗu na kashi ɗaya cikin ɗari.

Flash-Galerie Entwicklungshilfe Afrika
Hoton ɗaya daga cikin masu cin gajiyar taimakon raya ƙasa a Afirka.Hoto: picture-alliance/ZB

Shugabar kwamtin majalisar dokoki a fannin ayyukan taimakon raya ƙasa, Dagmar Wörhl daga jam'iyar CSU ta ce wannan ba hali ne da muke jin daɗinsa ba, to amma wajibi ne a lura da cewar Jamus a sakamakon mummunan rikicin kuɗi da tattalin arziƙi da ya addabi duniya baki ɗaya a yanzu, da farko sai ta fara gyara matsalar kasafin kuɗinta tukuna. A shekara ta 2010 kaɗai Jamus ɗin za ta ci bashin abin da ya kai Euro miliyan dubu 80. Ta ce "Idan mu kanmu muka fara rauni, to ba kuwa zamu iya taimaka wasu ba."

Kakakin jam'iyyar SPD a fannin taimakon raya ƙasa, Sascha Raabe, ya zargi ministan taimakon raya ƙasa, Dirk Niebel da laifin rashin ware isasshen kuɗi domin tafiyar da ayyukan raya ƙasa, duk kuwa da ganin cewar ƙasashen duniya sun sha daidaitawa kan haka a tarukansu dabam-dabam.Ya ce: "Ka ware kashi biyu cikin ukku ne kaɗai na kuɗin da aka tanadar yadda Jamus za ta sanya sunanta a ko'ina ake ayyukan agaji. Burinka ba shine a kyautata matsayin rayuwa a ƙasashe da ke fama da talauci ba, amma abin da ke kan gaba a gareka, shine ƙara yawan ƙwangilolin da kamfanonin Jamus suke samu a waɗannan ƙasashe. Ba kuwa zamu yarda da haka ba."

Dirk Niebel
Dirk Niebel, ministan raya ƙasashe masu tasowa.Hoto: AP

Babu shakka kuwa, ministan na taimakon raya ƙasa ya sanya alƙiblar manufofin ma'aikatarsa, inda yanzu yafi mai da hankali ga ƙara haɗin kai da kamfanonin Jamus. Lokacin muhawarar, shi kansa minista Niebel bai ce komai ba, ko da shike kakakin jam'iyyar CSU a ɓangaren taimakon raya ƙasa, Dagmar Wöhrl tace ministan yana sane da cewar samun ci gaba a fannin yaƙi da talauci yana tattare ne da kyautata matsayin rayuwa a yankunan karkara.

A madadin jam'iyyar nan ta masu neman canji, kakakinta, Niema Mossavat yace: "A ko wane daƙiƙa biyar yaro ke mutuwa saboda yunwa. Ya zuwa ƙarshen maganar nan tawa yara sittin ne zasu mutu.

Kakakin jam'iyyar Free Democrats, Christiane Ratjen-Damerau ta ce ba za'a ce manufofin taimakon raya ƙasa ƙarkashin shirin Millenium sun rushe gaba ɗaya ba ko kuma sun sami nasara gaba ɗaya ba. Duk da haka ta karematakan da minista Dirk Niebel yake ɗauka.Ta ce: "An sami nasarar rage yawan mace-mace daga cutar AIDS, an kuma rage yawan masu kasuwa da cutar. Kazalika, an sami nasarar ƙara yawan waɗanda ke samun isasshen ruwan sha mai tsabta. To amma gaba ɗaya ana iya an gano cewar shirin na Millenium baya tafiya cikin hanzari, yayin da ci gaban da aka samu a wasu fannoni kamar kula da lafiyar iyaye mata bai taka kara ya karya ba."

Gwamnatin Jamus har yanzu dai tana nan kan bakanta na cimma burin bayar da ɗigo bakwai cikin ɗari na kuɗin da take samu a shekara ga ayyukan taimakon raya ƙasa nan da shekara ta 2015. Wannan dai buri ne da ake son cimma sa tun shekara ta 1970, amma har yanzu bai samu ba.

Mawallafi: Marcel Fürstenau/Umaru Aliyu

Edita: Umaru Aliyu