1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin mata a yankunan rikici

March 4, 2005

Mata kan sha fama da wahala a yankunan da ake fama da rikice-rikice a cikinsu

https://p.dw.com/p/Bvcs

A taron hadin guiwa tsakanin wakilan gwamnatocin kasashe dabam-dabam da na majalisar dunkin duniya an duba halin da mata suka kasance a ciki a shekaru goman da suka wuce da kuma barazanar da suke fuskanta a kasashen da ake fama da rikici a cikinsu kamar Sudan da Irak da kuma Afghanistan. An ji daga bakin wani wakiliyar asusun Majalisar Dunkin Duniya akan raya makomar mata a kasar Sudan Ruth Kibiti tana cewa a hakika matan kan yi murmushi ne da ido daya sannan su rika kuka da daya idon. Ta ce a yayinda ake da zaman lafiya iya gwargwado a arewacin Sudan, ana ci gaba da zaman dar-dar a kudanci da kuma yammacin kasar, kuma mata sune suka fi shan wahala a wadannan rikice-rikice. Suna fama da cin mutunci da kuma barazana game da makomar rayuwarsu. Kitibi ta ce dole ne a dauke matakai na kasa da kasa domin kare lafiyar mata da yara a kasar Sudan. Dangane da kasar Afghanistan kuwa a yanzu al’amura sun fara sararawa bayan sama da shekaru goma da mata suka yi suna fama da danniya a karkashin mulkin Taliban, in ji Homa Sabri, wakiliyar asusun majalisar dunkin duniya mai kula da al’amuran mata UNIFEM a birnin Kabul. Dalilin wannan ci gaba kuwa shi ne zaman lafiya da kyatatuwar al’amuran tsaro a kasar Afghanistan. A cikin shekaru uku da suka wuce, tun bayan kifar da mulkin Taliban, matan ke bakin kokarinsu wajen inganta rayuwarsu a kasar, inda aka saba take hakkin mata, tun kafin ta fada cikin rikicinta na tsawon shekaru 20. Kungiyar neman ‘yancin mata ta kasar Afghanistan ta ce har yau a kan tsare mata a kurkuku saboda sun gudu daga gidajen mazajensu. Bugu da kari kuma har yau a kan ci mutuncin mata da fatacinsu a wannan kasa, wadda kimanin kashi casa’in cikin dari na matan ba su iya rubutu da karatu ba. A kasar Iraq kuwa, kamar yadda bayanai suka nunar danne hakkin mata abu ne da ya samo tushensa daga al’adun gargajiya, kamar dai a kasar Afghanistan. Da kyar a kan tura ‘ya’ya mata zuwa makaranta. Kuma mummunan ci gaban da ake samu shi ne sace-sacen matan da ake yi domin garkuwa da su, musamman masu shiga irin ta zamani, wadanda ba a girmama masu. Gaba daya wakilan sun bayyana fatan samun wata kyakkyawar hanya domin magance mummunan halin da mata ke ciki a yankunan da ake fama da rikici a cikinsu a duk fadin duniya.