1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsin lamba ga Rasha kan Aleppo

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 21, 2016

Kungiyar Tarayar Turai ta soki kasar Rasha dangane da halin taskun da fararen hula suka tsinci kansu a ciki, a birnin Aleppo na Siriya.

https://p.dw.com/p/2RVh3
Shugaban majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk
Shugaban majalisar Tarayyar Turai Donald TuskHoto: picture-alliance/AP Photo/G. Vanden Wijngaert

Shugabannin kungiyar da ke halartar wani taro kan yadda za su kara tsananta takunkuman karya tattalin arziki da suka sanyawa Rashan a birni Brussels na kasar Beljiyam, sun nunar da cewa sanya mata takunkumin zai taimaka wajen taka mata birki, a rawar da take takawa a yakin na Siriya. Koda yake shugaban majalisar Tarayyar Turan Donald Tusk ya ce ba fatansu ne su ci gaba da takun saka da Rashan ba yana mai cewa:

 

"Ci gab da takun saka da Rasha ba shi ne burinmu ba. Muna mayar da martani ne kawai kan matakan da Rasha ke dauka. Ko yaushe EU a shirye take ta zauna kan teburin tattaunawa, sai dai bama saba ka'idojinmu. Wannan ne ya sanya muke tsayawa kan matsayarmu cikin hadin kai. Kungiyar Tarayyar Turai EU na yin kira ga Rasha kan ta gaggauta kawo karshen hare-harenta a Siriya. Muna iya daukar ko wanne irin mataki in har ta ci gaba. Mun kuma bukaci wakilanmu da su ci gaba da kokarinsu na shigar da kayan agaji."

 

A hannu guda kuma Rasha ta sanar da tsawaita tsagaita wutar da take yi a birnin Aleppon, da nufin bayar da damar shigar da kayan agaji ga masu bukata zuwa sa'o'i 11 a ko wacce rana, nan da tsahon wasu kwanaki hudu masu zuwa.