1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matuka jiragen Lufthansa za su janye yajin aiki

November 26, 2016

Duk da cewar kungiyar matuka jiragen Lufthansa sun yi watsi da tayin da aka musu, sun yi alkawarin kin fadada yajin aikin da suka shiga.

https://p.dw.com/p/2TIIr
Deutschland Lufthansa-Pilotenstreik in Frankfurt
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Dedert

Sabon tayin na Lufhansan na da nufin warware takaddama da matuka jiragen, da ke yajin aiki tun daga ranar Laraba. Yajin aikin na wannan makon wanda ke zama na 14 irinsa kama daga shekara ta 2014, ya gurgunta ayyukan kamfanin da ya soke jirage wajen 2,600, batu da ya shafi pasinjoji sama da dubu 315.

Matuka jiragen na Lufhansa dai a baya, sun yi barazanar fadada yajin aikin nasu fiye da yau7 Asabar, batu daya haifar da damuwa a zukatan masu zuba jari, saboda dumbin asarar da kamfanin zai yi, dama barazanarsa ga tattalin arzikin Jamus da ke zama kasa mafi karfi a nahiyar Turai, a fannin tattali.

 A daren jiya Juma'a ce dai, kungiyar matuka jiragen na Lufthansa suka sanar da cewar, ba su da niyyar fadada yajin aikin fiye da yau Asabar.