1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mawuyacin Hali A Lardin Aceh Na Indonesiya

January 3, 2005

Talakawa 'yan rabbana ka wadata mu sun kara shiga mawuyacin hali na kaka-nika-yi a yankunan karkara na Lardin Aceh dake kasar Indonesiya.

https://p.dw.com/p/Bvdr
Mutane sun yi cincirindo domin karbar taimako a lardin Ache
Mutane sun yi cincirindo domin karbar taimako a lardin AcheHoto: AP

Duka-duka kason da aka shirya kayyade wa kowane mutum daya a mako bai zarce kilo daya na shinkafa ba, wanda dagacin kauyen Lawre dake da tazarar kilomitoci kalilan daga shelkwatar lardin Aceh ya ce ko kadan ba zai wadatar ba. Ya ce ambaliyar ruwan tayi awon gaba da dukkan abin da suka noma, kuma sai a jiya-jiyan nan ne aka fara kai musu taimakon abinci, wanda aka fara rarraba wa mutanen da suka yi cincirindo a gaban wata bukkar da aka kafa a tsakanin gidajen da ambaliyar tayi kaca-kaca da su. Matsalar ta kai intaha ganin cewar tuni da ma wadannan mutane matalauta ne ‚yan rabbana ka wadata mu, wadanda kuma ambaliyar ruwa tayi awon gaba da ‚yan abubuwan da suke mallaka. A lokacin da yake bayani Dr. Gideon Hartono cewa yayi:

Babbar matsalar da ake fama da ita ta shafi ruwan sha ne mai tsafta. A halin yanzu haka ruwan gishiri ya bannatar da ruwan da mutane suka saba aiwatarwa, sannan ga alamu kuma mai dake malalowa daga matatar dake nan kurkusa ya kara gurbata ruwan dake akwai. Wato dai ana fama da karancin ruwan sha mai tsafta. Kuma mai yiwuwa hakan ya kai ga kara yaduwar cutar gudawa da sauran cututtukan huhu.

Daya matsalar kuma shi ne yadda gurnati suka barbazu daga sansanin sojan dake kurkusa, wanda ambaliyar ruwan tayi kaca-kaca da shi. A saboda haka mutane ke dari-dari wajen kwashe sharar rusassun gidajen da suka yadu, saboda tsoron ka da wadannan nakiyoyi su yi bindiga su kuma yi awon gaba da mutum. Tuni da yawa daga mazauna kauyen na Lawre suka tsere zuwa wani tsauni dake wajen kauyen Ya-Allah ko ya zame musu tudun na tsira. Dagacin kauyen dai ya sikankance cewar mai yiwuwa su fara gina gidajke akan tsaunin saboda ba zasu sake yarda su koma da zama a bakin teku ba, musamman ma dangane da raderadin da ake yi na cewar akwai wata mahaukaciyar igiyar ruwan dake tasowa nan gaba kadan.