1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

May na son a takawa Koriya ta Arewa birki

Ahmed Salisu
August 30, 2017

Firaministar Burtaniya Theresa May ta yi kira ga hukumomin China da su kara yin matsin lamba ga Koriya ta Arewa kan ta daina yin gwajin makami mai linzami da ta ke yi.

https://p.dw.com/p/2j3vu
Nord Korea Kim Jong Un beim Test des Feststoffraketentriebwerks Pukguksong-2
Hoto: picture alliance/AP Photo/Korean Central News Agency

Firaminista May ta ce China na da rawar da za ta taka sosai wajen ganin an warware wannan batu na gwaje-gwajen makaman da Arewan ke yi wanda hakan inji ta ka iya tunzura wasu kasashen duniya. Wannan kira na May dai ta yi shi ne lokacin da ta ke kan hanyarta ta zuwa kasar Japan domin tattaunawa da Firaministan kasar Shinzo Abe. Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da mahukuntan Pyongyang suka yi wani gwaji na makami mai linzami wanda ya ratsa ta cikin Japan kana ya fada cikin Tekun Pacific.