1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan Boko Haram sun ba da kai a Nijar

December 28, 2016

Mayakan Kungiyar Boko Haram akalla guda 31 suka mika wuya ga hukumomin Jihar Diffa da ke fama da tashin hankalin na Boko Haram.

https://p.dw.com/p/2UyWR
Nigeria Boko Haram Terrorist
Hoto: picture alliance/AP Photo

Ministan cikin gida na Nijar Mohamed Bazoum ya sanar da cewar gomai a mayakan Kungiyar Boko Haram sun mika wuya ga hukumomin Jihar Diffa da ke gabashin kasar.Matasa 31 na Jihar ta Diffa da suka shiga rikicin na Boko Haram suka yanke shawarar mika wuya ga gwamnatin Nijar. Hakan kuwa na zuw ne kwanaki kalilan bayan da rundunar sojojin tarrayar Najeriya ta ba da sanarwa.
korar  Kungiyar na Boko Haram daga tungarsu ta dajin Sambisa.

Boko Haram
Hoto: Java

 Ana daf da kawo karshen Boko Haram bayan da rundunar sojojin Najeriya ta tarwatsasu daga dajin Sambisa

Yanzu haka dai kungiyoyin na masu fafutuka na ta bayar da shawarwari ga gwamnatin ta Nijar da cewar ta karbi matasan da suka yi saranda da hannu biyu wajen sake dawo da su cikin al'umma ta hanyar sama musu da ayyukan yi. Hare-haren wanda Kungiyar Boko Haram din ta soma kai wa tun a shekara ta 2009 sun yi sanadiyyar mutuwar mutane miliyan 15 kana wasu miliyan biyu suka ficce daga matsugunansu a kasashen Nijar da Najeriya da Kamaru da kuma Chadi.