1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan Islama sun janye daga Mogadishu yayin da dakarun Ethiopia ke dannawa a birnin

December 28, 2006
https://p.dw.com/p/BuWA
Dakarun Ethiopia da sojojin gwamnatin wucin gadi ta Somali na kara dannawa ga babban birnin kasar Mogadishu, wanda ke hannun mayakan sa kai na kotunan Islama. A wani taron hadin guiwa da suka yi a birnin Addis Ababa kungiyar tarayyar Afirka AU da ta kasashen Larabawa sun yi kira da a janye dakarun Ethiopia nan take kana kuma a kawo karshen rikicin tare da warware sa ta hanyar diplomasiya. Har yanzu kuwa kwamitin sulhu na MDD ya kasa cimma matsaya daya game da wani kuduri akan mummunar zubar da jinin da ke kara yin muni a kasar ta Somalia. Kamar a karon farko, har yanzu ana samun sabani akan wasu batutuwa da suka shafi dakarun ketare a Somalia. Yayin da kasar Qatar ke bukatar janyewar dakarun Ethiopia da sauran sojojin ketare su kuwa sauran membobi 14 na kwamitin sulhun na adawa ne da wannan bukata. A jiya sojojin Ethiopia sun ce ba zasu kutsa cikin birnin Mogadishu ba, to amma zasu yi masa kofar rago har sai mayakan sa kai na Islama sun yi saranda.