1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mdd na shirin mayar da yan gudun hijirar Angola zuwa gida

April 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3T

Hukumar kula da yan gudun hijira ta Mdd, tace tana nan tana shirin mayar da yan gudun hijirar kasar Angola dubu 12 dake zaman gudun hijira a Zambia.

A can baya dai a cewar Mdd an samu galabar mayar da yan gudun hijirar ta Angola dubu 63 izuwa gida da taimakon mahukuntan na Zambia a hannu daya kuma da kungiyoyin bayar da agaji.

Yan gudun hijirar dai a cewar hukumar ta Mdd sun tsere ne daga kasar ta Angola don tsira da rayukan su, bisa yakin basasa na tsawon shekaru 27 da kasar tasha fama dashi.

A cewar kakakin hukumar kula ta yan gudun hijirar ta Mdd, wato Kelvin Shimo, hukumar ta shirya kashe dalar Amurka miliyan 4 da digo 7 ne don gudanar da wannan aiki.

Bugu da kari kakakin hukumar ya kuma tabbatar da cewa hukumar ta yan gudun hijira ta shirya gudanar da wannan aikin ne a cikin wannan shekara ta 2006 da muke ciki.