1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hasashen rudani a arewa maso gabashin Najeriya

February 16, 2017

Karewar wa'adin kungiyoyin agaji rudanin arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/2XixS
Nigeria Stadt Borno State
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Najeriya na iya shiga rudani a bangaren kyautata al'umura a shiyar arewa maso gabashin kasar, muddin kungiyoyin agaji suka gaza cimma tasiri a cikin watanni 18 da suka rage masu.

Jagoran shirin samar da agaji na MDD a Najeriya Edward Kallon, ya ce da sauran aiki ta fuskar daidaita al'amura a shiyar da ta fuskanci tsananin ta'asar mayakan Boko Haram shekaru 7 da suka gabata.

Jami'in na MDD ya kuma ce ko a bara ma sun fuskanci matsalar karancin kudaden samar da agaji, yayin kuma da a bya-bayan nan, shirin samar da abinci na duniya ya hasaso yiwuwar fuskantar bala'in yunwa.

A halin ma da ake ciki akwai aklla yara kanana dubu 45 da za su iya fuskantar karancin abincin da suke bukata, in har babu tsayeyyen matakin da aka dauka

Sama da mutane dubu 20 ne dai suka salwanta, yayin da wasu miliyan 2 da rabi suka rasa matsugunai sakamakon ayyukan Boko Haram a Najeriya.