1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta ja hankalin Najeriya kan 'yan Chibok

July 25, 2017

Majalisar Dinkin Duniya, ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi kokarin ceto sauran 'yan matan makarantar Chibok da mayakan Boko Haram ke ci gaba da rakuwa da su.

https://p.dw.com/p/2h7It
Nigeria - Heimkehr der Chibok Mädchen
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Fiye da 'yan mata na makarantar Chibok 100 ne dai ke hannun mayakan na Boko Haram, bayan kwashe su kimanin 270 da suka yi cikin watan Afrilun shekara ta 2014, a yankin arewa maso gabashin Najeriyar.

Wata tawagar kwararru ta bai wa MDD shawarin cewa wajibi ne a tabbatar da an bai wa mata da 'yan matan da Boko Haram ke garkuwa da su,  cikakkiyar kulawar da za ta kyautata tunaninsu ta yadda za su iya sajewa da jama'a ba tare da samun matsala ba.

Sama da mutum dubu 20 ne dai tarzomar ta Boko Haram ta halaka tare da raba wasu sama da miliyan 2 da sukuni, cikin tsukin shekaru bakwai na yakin da suke ikirarin na kafa daula a nahiyar Afirka.